Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kungiyoyin Premier League za su yi aman fam miliyan 340
An sanar wa da kungiyoyin Premier League cewar za su mai do da fam miliyan 340, kudin nuna wasanni a talabijin idan za a ci gaba da kakar bana ba tare da 'yan kallo ba.
A ranar Litinin jami'an kungiyoyin Premier suka yi taro don zakulo hanyar da ya kamata a karkare kakar 2019-20.
Shugabannin sun ce an yi watsi da batun kammala kakar bana a wasu filayen, za kuma su sanar da mahukuntan gasar Premier domin su sake shawara.
Kungiyoyin za su mayar da kudin ne, bayan da za a ci gaba da wasannin ba kamar yadda aka tsara ba tun kan bullar cutar korona.
Haka kuma za a ci gaba da wasannin ba tare da 'yan kallo ba, kuma ba lokutan da aka amince da su wajen nuna gasar ba. .
An yi kiyashin cewar kungiyoyin da ke buga gasar Premier za su samu fam biliyan 9.2 kudin tallata wasannin a kafafen yada labarai tun daga kakar 2019 zuwa 2022.
A baya can shugaban gudanar da wasannin Premiel League, Richard Masters ya yi hasashen za a yi hasarar fam biliyan daya idan aka kasa karkare kakar wasa ta 2019-20.
Cikin watan Maris aka dakatar da gasar cin kofin Premier ta bana a lokacin da Liverpool wadda rabonta da kofin tun shekara 30 ke mataki na daya a kan teburi da tazarar maki 25.