Coronavirus: 'Yan Brighton uku na dauke da cutar korona

An samu dan kwallon Brighton na uku dauke da cutar korona.

Ba a bayyana sunan dan kallon ba, wanda ya killace kansa, bayan da aka yi masa gwaji ranar Asabar - tun a baya ne aka samu 'yan kwallon Brighton biyu dauke da annobar.

'Yan wasan Brighton na yin atisaye a daidaiku, kuma kungiyar ta ce haka za su ci gaba da yi zuwa wani lokaci.

Ranar Litinin mahukuntan gasar Premier za su yi taro don ci gaba da neman hanyar da za a karkare kakar 2019-20.

A ranar 13 ga watan Maris aka dakatar da dukkan wasannin cin kofin Premier na bana don gudun yada cutar korona.

Mahukunta na sa ran ci gaba da wasanni cikin watan Yuni, amma ba tare da 'yan kallo ba.

Saura wasa tara a kammala gasar shekarar nan, kuma Liverpool ce ta daya a kan teburi da tazarar maki 25 tsakaninta da Manchester City ta biyu.