Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Babu ranar kammala gasar Premier ta bana
Kungiyoyin Premier sun ce za su kammala wasa 92 da suka rage musu a kakar wasa ta bana ko da yake basu tattauna kan ranar da za a ci gaba da gasar ba a taron da suka gudanar ranar Juma'a.
An yi tsammanin kungiyoyin za su tattauna kan wa'adin ranar 30 ga watan Yuni da aka sanya domin ci gaba da tamaula amma sai kawai suka yi muhawara kan "yiwuwar sauya tsarin" gasar.
Hukumar Gasar Premier ta ce "babban burinmu shi ne" mu kammala wasannin amma a halin yanzu "dukkan ranakun ba a da tabbas" a kansu.
Ranar 13 ga watan Maris aka dakatar da gasar Premier saboda annobar coronavirus.
An yi ammanar cewa wasu kungiyoyin sun so tattaunawa kan wa'adin ranar 30 ga watan Yuni a taron na ranar Juma'a amma an bayyana cewa yanzu ba lokaci ba ne da za a yi irin wannan tattaunawa.
"Kamar yadda yake a kasuwanci da masana'antu, ita ma Hukumar Gasar Premier da kungiyoyin da ke gasar suna aiki cikin tsare-tsare masu tsauri," in ji Hukumar Premier.
Wanne hali a sauran gasar da ake yi a Turai?
Gasar Bundesliga ta Jamus: Kungiyoyi sun koma atisaye ko da yake har yanzu ba a koma kakar wasa ta bana ba sai ranar 30 ga watan Afrilu.
Gasar La Liga ta Spaniya: Ba za a ci gaba da atisaye ba sai an janye dokar ta-baci kuma shugaban La Liga Javier Tebas ya ce komawa wasa ranar 28 ga watan Mayu shi ne mafi a'ala.
Gasar Ligue 1 ta Faransa: Hukumomin kwallon kafar Faransa na duba yiwuwar sake gasar Ligue 1 ranar 3 ko 17 ga watan Yuni, inda take ganin ranar 17 din ta fi zama tabbas, a cewar sports daily L'Equipe.
Gasar Serie A ta Italiya: Hukumomin kwallon kafar Italiya tana fatan soma yi wa 'yan wasa gwajin coronavirus a farkon watan Mayu, domin shiryawa ci gaba da kakar wasan.