Manchester United na son dauko Bellingham, Everton na zawarcin Grealish

Manchester United ce a sawun gaba wajen kokarin dauko dan wasan Birmingham mai shekara 16 Jude Bellingham wanda za a sayar a kan £35m. Su ma Chelsea da Borussia Dortmund suna zawarcin Bellingham. (Sun)

Wakilin dan wasan Real Madrid da Colombia James Rodriguez, mai shekara 28, ya tuntubi Manchester United domin yiwuwar komawar dan wasan Old Trafford a bazara. (Sport via Metro)

Everton za ta iya yunkurin dauko dan wasan Aston Villa Jack Grealish, mai shekara 24, idan sun kammala dauko manyan 'yan wasa. Chelsea kuma tana son dauko dan wasan Gremio da Brazil Everton Soares, mai shekara 24. (Sky Sports)

Kazalika an samu ci gaba a yunkurin da Everton take yi wajen dauko dan wasan Lille dan kasar Brazil Gabriel Magalhaes. Chelsea da Arsenal sun so dauko dan wasan mai shekara 22.(Guardian)

Haka kuma, Everton tana son sayo dan wasan Lazio da Italiya Ciro Immobile, mai shekara 30 - sannan tana so ta bayar da Moise Kean, mai shekara 20, a wani bangare na karbo Immobile. (Teamtalk)

Liverpool tana tattaunawa da zummar dauko dan wasan Inter Milan da Croatia Marcelo Brozovic, mai shekara 27. (Libero via Express)

Real Madrid ta shirya tsaf domin rike dan wasan da Arsenal take son dauka Luka Jovic. Sau daya kacal dan kasar ta Serbia, mai shekara 22, ya buga cikakken wasa a Real a kakar wasa ta bana. (Sport via Sun)

Celtic ta tuntubi Manchester City domin yiwuwar sake dauko Patrick Roberts a kan £3m. A baya dan wasan mai shekara 23, wanda ke zaman aro a Middlesbrough, ya yi zaman aro na tsawon kakar wasa biyu a Celtic. (Teamtalk)

Barcelona na sa ran dawo da dan wasan Brazil Philippe Coutinho a kakar wasa mai zuwa, a cewar koci Quique Setien. Ana rade radin cewa Chelsea da Tottenham suna son dauko dan wasan mai shekara 27, wanda ke zaman aro a Bayern Munich. (Evening Standard)

Dan wasan Italiya Federico Chiesa zai iya barin Fiorentina Idan aka taya shi a kan farashi mai armashi, a cewar shugaban kungiyar. Manchester United, Juventus da Inter Milan suna zawarcin dan wasan mai shekara 22. (Sky Italia - in Italian)

Shahararren dan wasan Jamus Lothar Matthaus ya bai wa dan wasan baya na RB Leipzig Dayot Upamecano shawarar ci gaba da zama a kungiyar. Arsenal da Manchester United suna son dauko dan wasan na Faransa, mai shekara 21. (Evening Standard)

Dan wasan Barcelona Nelsom Semedo ya dakatar da tattaunawar da yake yi da kungiyar kan yiwuwar sabunta kwantaraginsa. Dan kasar ta Portugal, mai shekara 26, yana so ya samu tabbacin cewa za a rika sanya shi a wasa akai-akai kafin ya sabunta kwangilar tasa. (Sport - in Spanish)

'Yan wasan Arsenal suna dab da amincewa a rage 12.5% na albashin da ake ba su wata-wata domin a samu kudin yaki da cutar korona. (The Athletic - subscription required)