Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar musayar 'yan ƙwallo: Makomar Grealish, Dyche, Zaniolo, McNeil, Jimenez
Manchester United za ta biya £80m a kan dan wasan tsakiya na Aston Villa Jack Grealish, mai shekara 24, ko da kuwa kungiyarsa ta faɗo daga matakin gasar Premier. (Mirror)
Manchester Unitedtana zawarcin dan wasan Bayern Munich Corentin Tolisso kuma kungiyar ta Jamus ta shirya barin dan wasan mai shekara 25 dan kasar Faransa ya tafi domin ta samu kudin sayo wasu 'yan wasan, cikinsu har da dan wasan Manchester City da Jamus Leroy Sane, 24. (Express)
Juventus za ta fafata da Manchester United a yunkurin dauko dan wasan Wolves Raul Jimenez, mai shekara 29. (Times - subscription required)
An yi ammanar cewa dan wasan Bournemouth da Scotland Ryan Fraser, mai shekara 26, yana son komawa Tottenham idan kwangilarsa ta kare ranar 30 ga watan Yuni. (Mirror)
Liverpool ta bai wa Pedro Chirivella, mai shekara 22, karin kwangilar shekara biyar amma har yanzu bai yanke shawara kan makomarsa ba, domin kuwa Nantes da Rangers suna zawarcinsa. (Goal)
Liverpool tana son dauko dan wasan Roma Nicolo Zaniolo, mai shekara 20, wanda Manchester United da Tottenhamsuke zawarci da bazara. (Corriere dello Sport - via Sports Mole)
A gefe guda, an yi ikirarin cewa da ma Liverpool ta yi yunkurin dauko Zaniolo kafin annobar korona ta tilasta wa kungiyoyin kwallon kafa dakatar da tamaula. (Il Tempo - in Italian)
Dan wasanReal Sociedad Diego Llorente, mai shekara 26, yana so ya bar kungiyar a azara kuma an ce Monaco da Liverpool suna cikin kungiyoyin da ke son dauko shi. (La Razon - Spanish)
Crystal Palace tana shirin sayo mutum uku daga Burnley, wadanda suka hada da kocinsu Sean Dyche, da 'yan wasa Dwight McNeil, mai shekara 20, da James Tarkowski, dan shekara 27. (Mirror)
Dan wasanFiorentina Christian Koffi, dan shekara 19, ya yanke shawarar kin komawa Liverpool a 2018 amma ya ce hakan ba kuskure ba ne. (sofoot - in French)