Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hukumar kwallon kafar Turai ta tsara yadda za ta karkare kakar 2019-20
Shugaban hukumar kwallon kafar Turai, Uefa, Aleksander Cerefin ya ce sun tsara hanyoyin da za su bi don kammala wasannin bana a cikin watan Agusta.
A baya BBC ta bayar da rahoton cewar a cikin watan Agusta za a kammala gasar Champions League da ta Europa League.
Ana sa ran buga wasannin gida da waje a matakin daf da na kusa da na karshe.
Cefarin ya ce za a buga wasannin ne ba 'yan kallo, kuma yana fatan mambobinta za su karkare gasarsu ta bana.
Ranar 13 ga watan Maris aka dakatar da gasar Champions League da ta Europa League da Premier League da sauran wasanni saboda bullar cutar korona.
Shugaban ya kara da cewa duk kasar da ba ta kammala gasar 2019-20 ba, za ta shiga wasannin neman gurbin buga gasar zakarun Turai ta badi kenan.
Ranar 12 ga watan Yuni aka tsara buga gasar Euro 2020 a kammala 12 ga watan Yuli, amma yanzu za a fara daga 11 ga Yuni zuwa 11 Yulin 2012.
Tun a baya ne a cikin watan Maris aka cimma wannan matsaya don gudun yada cutar korona.
Za a gudanar da wasannin daf da na karshe na Uero 2020 a Wembley, tare da sauran kasashen da ke karbar bakuncin wasannin da suka hada da Amsterdam da Baku da Bilbao da Bucharest da Budapest da Copenhagen da Dublin da Glasgow da Munich da Rome da kuma St Petersburg.