Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Uefa za ta sanar da yadda za a karkare wasannin kakaf bana
- Marubuci, Simon Stone
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, Uefa za ta bayyana shirin yadda za a kare kakar bana ta 2019-20, inda za ta yi taro da mambobinta 55 ta bidiyo ranar Talata.
Uefa na fatan a kammala wasanni cikin watan Agusta, inda hukumar ta raba wasu mahukunta gida biyu, inda za a tantance kalandar wasanni. Ana sa ran tsayar da takamaimiyar ranar karkara wasanni zuwa tsakiyar Mayu a kalla.
Sai dai kuma koma bayan da cutar da korona ta jawo ya sa an samu matsaloli a wasu manyan gasar Turai - kamar Jamus da Denmark - suna sa ran ci gaba da wasanni a wata mai zuwa. Yayin da a Ingila da sauran kasashe na cewar kamata ya yi a fara wasanni a watan Yuni idan komai ya lafa - wasu kungiyoyin Premier na ganin lokacin ya haura hakan.
Uefa na fatan kammala wasanninta na Champions da na Europa League kamar yadda ta saba na gida da waje. Sai dai an fahimci hakan zai yi wahala ganin lokaci ya kure, har ma wasu na cewa a mayar da wasannin na karamar gasa daga kungiyoyin da suka rage a karawar daf da na kusa da na karshe a wasannin.
Bayan taron da hukumar kwallon Turai za ta gabatar ranar Talata, ranar Alhamis kuma kwamitin amintattu zai gabatar da nasa taron don amincewa ko akasin hakan kan shawarar da ake yanke ranar Talata