Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Uefa ta bukaci mambobinta su fada mata ko za su iya kare kakar bana
Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, Uefa ta bukaci mambobinta daga nan zuwa 25 ga watan Mayu su sanar da ita ko za su iya karkare kakar 2019-20.
An dakatar da dukkan wasannin kwallon kafa a nahiyar Turai cikin watan Maris saboda tsoron yada korona, in banda Belarus da ta ci gaba da fafatawa.
A wannan makon ake sa ran masu ruwa da tsaki za su yi taro don fitar da hanyoyin da za a bi a ci gaba da gasar Premier.
Arsenal da Tottenham da Brighton da kuma West Ham sun bude wajen atisaye amma bisa tsarin da gwamnati ta gindaya na bayar da tazara.
Ana sa ran ci gaba da gasar Premier ranar 6 ga watan Yuni a karkare a karshen Yuli, inda ake sa ran kungiyoyi su koma atisaye cikin rukuni ranar 18 ga watan Mayu.
Manyan kungiyoyin Premier za su zauna taro ranar Juma'a domin fitar da matsaya kan yadda ya kamata a karkare kakar 2019-20.
Uefa ta bukaci mambobinta da su yi duk abin da ya dace domin kammala wasannin bana, domin samun kungiyoyin da za su shiga gasar Zakarun Turai ta badi.