Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Silva zai tsawaita zamansa a Manchester City, Manchester United za ta ɗauko Matondo
Kwangilar dan wasan tsakiya David Silva a Manchester City za ta kare ranar 30 ga watan Yuni, amma dan kasar Spaniya, mai shekara 30, ya shirya tsaf don tsawaita zamansa a kungiyar zuwa karshen kakar wasa ta bana. (Times - subscription required)
Manchester United tana sanya ido kan dan wasan Schalke dan kasar Wales Rabbi Matondo kuma za ta iya soma zawarcin dan wasan dan shekara 19 idan bata yi nasarar dauko dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20 ba. (Manchester Evening News)
Dan wasan daChelsea take son daukowa Dries Mertens zai ci gaba da zama a Napoli idan kwangilarsa ta kare, a yayin da Inter Milan take sha'awar sayo dan kasar ta Belgium mai shekara 33. (Mail)
Dan wasan Bayern Munich da Poland Robert Lewandowski, mai shekara 31, ya shawarci dan wasan Norway dan shekara 19 Erling Braut Haaland - wanda ake rade radin zai koma Manchester United ko Real Madrid - da ya ci gaba da zama a Borussia Dortmund. (Metro)
Wakilin Philippe Coutinho ya ce dan wasan na Brazil bai tattauna da kowacce kungiya ba game da dan wasan na Barcelona mai shekara 27, wanda yake zaman aro a Bayern Munich. (Talksport)
Za a sayar da dan wasanSouthampton Che Adams a bazara a kan £10m ko kasa da haka - duk da cewa Leeds United ta amince ta biya £19m a kan dan kwallon dan shekara 23 a watan Janairu amma daga bisani ta sauya janye. (Football Insider)
Dan wasanManchester United dan shekara 19 mai buga gasar Under-20 Angel Gomes, wanda kwangilarsa za ta kare a kungiyar a bazara, bai sabunta kwangilarsa ba saboda shakkar da yake yi game da yiwuwar sanya shi a babbar kungiyar da kuma zargin United da yunkurin dauko wasu 'yan wasa sa'anninsa. (Manchester Evening News)
Leeds United za ta iya yunkurin dauko dan wasan TottenhamHotspur da Argentina Juan Foyth, dan shekara 22, idan suka samu matsayi zuwa Gasar Firimiya. (Football Insider)