Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Werner, Sane, Dembele, Bakayoko, Bellingham, Havertz
Shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya bayyana matukar mamakinsa bayan dan wasan Jamus da RB Leipzig dan shekara 24 Timo Werner, wanda ake rade radin zai koma Chelsea, Liverpool ko Manchester United, ya ce ya gwammace komawa kasashen waje maimakon zaman Jamus. (Bild, via Metro)
Bayern Munich tana duba yiwuwar ware fiye da £50m domin dauko Manchester City Leroy Sane, a yayin da kwangilar dan wasan na Jamus mai shekara 24 take shirin karewa a karshen kakar wasa ta bana. (Telegraph)
Manchester United ta samu damar sayen dan wasan Faransa da Lyon mai shekara 23 Moussa Dembele, wanda kuma Chelseata so dauko shi, a kan £61.8m. (Todofichajes, via Express)
Manchester United tana son dauko dan wasa mai shekara 16 Jude Bellingham domin saka shi a cikin manyan 'yan wasa idan suka sayo shi daga Birmingham City a bazara. (Evening Standard)
Chelsea tana shirin sayar da dan wasan Faransa Tiemoue Bakayoko, mai shekara 25, a kan £31m amma Paris St-Germain ba ta son sayensa a kan sama da £26.5m. (Le10 Sport, via Star)
Barcelona za ta sallama dan wasan Faransa Ousmane Dembele dan shekara 22 a kan £53m wanda ta sayo a kan£135.5m. (Marca, via Star)
An yi wa kungiyoyin kwallon kafa tayin sayen dan wasanTottenham Juan Foyth kuma Barcelona tana sha'awar sayen dan wasan na Argentina mai shekara 22. (Mirror)
Barcelona ta tattauna da Juventus a kan sayen dan wasan Italiya Mattia de Sciglio, dan shekara 27, daga kungiyar wacce take buga gasar Serie A bayan tattaunawarsu da dan wasan Portugal Nelson Semedo, dan shekara 26, ta wargaje. (Marca)
Ana rade radin dan wasan Bayer Leverkusen Kai Havertz, dan shekara 20, zai koma Chelsea, Liverpool ko kuma Manchester United sai dai tsohon dan wasan Jamus Michael Ballack ya ba shi shawara kada ya bar kungiyar da yake a yanzu. (Football London)
Everton tana shirin barin golan Netherlands Maarten Stekelenburg, mai shekara 37, ya bar kungiyar idan kwangilarsa ta kare a karshen kakar wasa ta bana sannan ta dauko sabon dan wasa wanda zai fafata da golan Jordan Pickford, mai shekara 26. tFootball Insider).