Coronavirus: Za a ci gaba da Bundesliga in ji Angela Merkel

Bayern Munich

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bayern Munich ce kan gaba a teburin Bundesliga da tazarar maki hudu

Angela Merkel ta tabbatar da cewar za a ci gaba da gasar Bundesliga cikin watan nan don karkare kakar 2019-20.

Gasar za ta zama ta farko da za a ci gaba da fafatawa a nahiyar Turai, ana sa ran ranar Alhamis hukumar kwallon kafar Jamus za ta sanar da ranar da za a ci gaba da wasannin a watan nan.

Sai dai kuma dukkan wasannin za a yi sune ba 'yan kallo.

Saura wasa tara a karkare kakar shekarar nan, inda Bayern Munich ke mataki na daya da tazarar maki hudu tsakaninta da Borrusia Dortmund.

Wannan batun ya zo ne bayan da aka samu 'yan wasa 10 da ke buga gasar Jamus dauke da cutar korona, bayan gwajin 'yan kwallo 1,724 da aka yi.

A makon jiya ne 'yan wasa suka fara atisaye, bayan da mahukuntan gasar Jamus suka sa ran ci gaba da wasannin kakar bana ranar 9 ga watan Mayu.

Gwamnatin Jamus ta hana taron jama'a a waje daya har sai 24 ga watan Oktoba - Saboda haka ne za a ci gaba da wasannin ba tare da 'yan kallo ba.