An jinkirta hukunci kan buga gasar Bundesliga ta Jamus

Asalin hoton, Getty Images
Za a kara jira na mako guda kafin a sani ko zai yiwu a koma buga gasar Bungesliga ta Jamus, a yayin da gwamnati ta jinkirta yanke shawara kan batun.
Tun a tsakiyar watan Maris aka dakatar da gasar saboda annobar korona.
Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce duk wani hukunci a kan batun komawa buga wasanni ba za a yanke ba har sai zuwa ranar 6 ga watan Mayu.
"Akwai bukatar mu jajirce kuma mu bi dokokin kiwon lafiya," in ji Merkel.
Hukumar kwallo Jamus (DFL) ta yi gargadin cewa manyan kungiyoyi a gasar za su shiga cikin matsalar kudi idan ba a koma tamaula ba a watanYuni.

Asalin hoton, Getty Images
Sauran wasanni tara a kammala gasar, kuma Bayern Munich ce a saman tenur inda ta baiwa Borussia Dortmund ta zarar maki hudu.







