Cutar korona: Ba a samu karin masu dauke da cutar a FC Cologne ba

FC Cologne

Asalin hoton, Getty Images

Ba a samu karin wadanda suka kamu da cutar korona a FC Cologne ba, bayan da 'yan wasanta uku suka kamu da cutar a makon jiya.

Tuni kuma kungiyar ta ci gaba da yin atisaye cikin rukuni-rukuni kamar yadda gwamnati ta umarta, a shirin da ake na ci gaba da gasar Bundesliga ta bana.

Kungiyar ta ce kawo yanzu 'yan kwallon uku ba sa dauke da annobar, amma an killace su zuwa kwana 14, kuma ba za a sake gwada su ba idan wa'adin ya cika.

Bundesliga na shirin zama ta farko da za ta ci gaba da wasannin tamaula a Turai, domin karkare kakar 2019-20.]

Mahukunta na fatan ci gaba da fafatawa ranar 9 ga watan Mayu, sai dai gwamnati ta bukaci a jinkirta, watakila a koma wasanni ba tare da 'yan kallo ba ranar 16 ko kuma 23 ga watan Mayu.

Gwamnatin Jamus za ta zauna taro da masu ruwa da tsaki ranar Laraba 6 ga watan Mayu domin fayyace ranar da ya kamata a ci gaba da gasar Bundesliga shekarar nan.

Saura wasannin tara suka rage a karkare gasar Jamus, inda Cologne ke mataki na tara a kan teburi.