An bukaci Aubameyang ya bar Arsenal

Pierre Emerick-Aubameyang

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Pierre Emerick-Aubameyang ya samu kyautar takalmin zinare tare da 'yan Liverpool,Mohamed Salah da Sadio Mane a kakar wasan da ta wuce.

Shugaban hukumar kwallon kasar Gabon, ya bukaci dan kwallon Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang "ya koma wata kungiya da ke da tsarin samun nasarori".

Dan wasan ya yi kan-kan-kan tare da wasu 'yan kwallon a matsayin wadanda suka fi zura kwallaye a gasar Premier a kakar wasan da ta wuce, inda ya ci kwallo 22.

A kakar wasa mai zuwa ne kwangilarsa za ta kare a Arsenal.

"A yanzu yana Arsenal, bai ci kowanne kofi ba,"Pierre Alain Mounguengui ya shaidawa ESPN.

Mounguengui ya kara da cewa " Idan Pierre ya samu wata kungiya, gwamma ya kara gaba."

A watan da ya wuce, kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ce yanason Aubameyang ya ci gaba da murza leda a Gunners 'kota hallin kaka'.

A watan Janairun 2018, Aubameyang ya koma Arsenal daga Borussia Dortmund a kan fan miliyan 56.