Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An bukaci Aubameyang ya bar Arsenal
Shugaban hukumar kwallon kasar Gabon, ya bukaci dan kwallon Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang "ya koma wata kungiya da ke da tsarin samun nasarori".
Dan wasan ya yi kan-kan-kan tare da wasu 'yan kwallon a matsayin wadanda suka fi zura kwallaye a gasar Premier a kakar wasan da ta wuce, inda ya ci kwallo 22.
A kakar wasa mai zuwa ne kwangilarsa za ta kare a Arsenal.
"A yanzu yana Arsenal, bai ci kowanne kofi ba,"Pierre Alain Mounguengui ya shaidawa ESPN.
Mounguengui ya kara da cewa " Idan Pierre ya samu wata kungiya, gwamma ya kara gaba."
A watan da ya wuce, kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ce yanason Aubameyang ya ci gaba da murza leda a Gunners 'kota hallin kaka'.
A watan Janairun 2018, Aubameyang ya koma Arsenal daga Borussia Dortmund a kan fan miliyan 56.