Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tsohon dan Liverpool Dalglish ya kamu da coronavirus
Tsohon gawurtaccen dan kwallon Liverpool, Sir Kenny Dalglish ya kamu da cutar coronavirus kuma yanzu haka yana kwance a asibiti.
Sanarwar da iyalansa suka fitar, ta ce tun a ranar Laraba aka kwantar da Dalglish a asibiti kuma ana yi masa karin ruwa.
Dan shekaru 69, wanda ya buga wa Celtic da Scotland kwallo, ya kamu da cutar ce bayan da aka kwantar da shi saboda wata cutar ta daban.
Dalglish ya lashe kofi takwas a Liverpool a matsayinsa na koci da kuma dan wasa, sannan kuma ya lashe kofunan zakarun Turai uku.
Sannan kuma a shekarar 1995, ya lashe kofin Premier tare da Blackburn Rovers.