Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaha ya gayyaci masu yaki da coronavirus su je gidansa su zauna
Hukumar gasar Firimiya za ta sake gudanar da bincike kan rahotannin da ke cewa wasu kungiyoyin kwallon kafa suna buga wasanni a bayan fage domin su kammala kakar wasa ta bana duk da yaduwar da coronavirus ke ci gaba da yi. (Independent)
Manchester United na tattaunawa da dan wasan tsakiyarta Nemanja Matic, mai shekara 31, a kan sabon kwantaragin shekara biyu inda za a rika biyansa £140,000 duk mako lamarin da zai sa dan wasan na Serbia ya tsawaita zamansa da shekara daya. (Sun)
Dan wasan Crystal Palace dan kasar Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekara 27, ya yi wa hukumar kula da lafiya ta Birtaniya tayin gidajensa 50 domin ta bai wa ma'aikatanta da ke aiki a asibitocin tsakiyar London wadanda ke yaki da coronavirus su rika kwana a ciki. (Times - subscription required)
Dan wasan West Brom Charlie Austin ya gargadi mutane cewa su daina daukar coronavirus da wasa bayan an tabbatar yana dauke da kwayar cutar. Dan wasan mai shekara 30 yana zargin cewa ya harbu da cutar ne lokacin bikin Cheltenham. (Telegraph - subscription required)
Dan wasan Chelsea Willian, mai shekara 31, ya nemi kungiyar ta ba shi izinin ya koma kasarsa Brazil domin ya gana da iyalinsa. (Mirror)
Liverpool ta kwashe "tsawon lokaci" tana tattaunawa da dan wasan Lille mai shekara 21Boubakary Soumare. (Sport - in Spanish)
Dan wasan Sassuolo Jeremie Boga, mai shekara 23, zai iya komawa Chelsea saboda ka iya biyansa £12.8m. (Mail)
Juventus tana son bai wa Chelsea dan wasan Bosnia-Herzegovina Miralem Pjanic, mai shekara 29, a wani bangare na musayar da za su yi domin ta karbo dan wasan Italiya mai shekara 28 Jorginho. (Corriere dello Sport, via Sun)
Dan wasan da Manchester United ta karbi aro Odion Ighalo, mai shekara 30, yana karba £8,000 kan duk kwallo guda daya da ya zura da kuma £9,000 a duk lokacin da kungiyar ta yi nasara a wasa baya ga alawus din £180,000 a duk mako a Old Trafford. (Sun)
Barcelona da Real Madrid na iya zawarcin dan wasan Austria mai shekara 27 David Alaba, wanda ba shi da tabbaci zai sabunta kwantaraginsa a Bayern Munich.(Bild - in German)