Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Watakila a ci gaba da gasar La Liga a watan Mayu
Shugaban gasar La Liga, Javier Tebas ya ce watakila a ci gaba da wasannin a Spaniya ranar 28 ga watan Mayu kamar yadda suke tattaunawa.
Babu wata kungiyar kwallon kafar Spaniya da ke buga gasa tun bayan da Atletico Madrid ta fitar da Liverpool daga Champions League ranar 11 ga watan Maris.
Tebas ya ce babu wata kungiya da za ta yi atisaye har sai an dauki matakan da suka kamata don gudun yada coronavirus.
Tun farko mahukuntan kwallon kafa a Spaniya sun tsayar da ranar 26 ga watan Afirilu domin ci gaba da wasanni a kasar, bayan da aka dakatar da dukkan harkokin tamaula a cikin watan Maris.
Shugaban gasar La Liga ya yi kiyashin cewar kungiyoyin Spaniya za su yi hasarar yuro biliyan daya idan har aka soke wasannin kakar bana.
Tebas ya ce suna tattauna wa da Uefa kan ranaku uku da ya kamata a koma ci gaba da La Liga da ya hada da 28 ga watan Mayu ko kuma 6 ga watan Yuni ko kuma 28 ga watan na Yunin.