Ceballos zai iya tsawaita zamansa a Arsenal, Wilson na shakku kan Firimiya

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Bournemouth Callum Wilson, mai shekara 28, ya ce bai cancanci a alakanta shi da manyan kungiyoyin Gasar Firimiya ba saboda ba shi da koshin lafiya a kakar wasa ta bana. (Sky Sports)
Dan wasan Gent da Canada Jonathan David, mai shekara 20, ya ce nan gaba yana so ya fafata a Gasar Firimiya. (Guardian)
Dan wasan Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 30, da takwaransa na Manchester City Leroy Sane, mai shekara 24, na cikin 'yan wasan da ke bata ran kungiyoyin Firimiya game da tsawaita kwangilarsu bayan an matso da wa'adin musayar 'yan wasa baya. (Telegraph)
Dan wasan Wolves da Mexico Raul Jimenez, mai shekara 28, ya bayyana cewa ba a sanya masa farashi ba, a yayin da ake cewa Manchester United da Real Madrid suna zawarcinsa. (Marca, via Mail)
An sanya dan wasan Spain Dani Ceballos, mai shekara 23, a jerin 'yan wasan da ba a sa su buga tamaula a Real Madrid, lamarin da ya bai wa Arsenal damar soma zawarcinsa. (Mirror)
An gaya wa dan wasan tsakiya na Aston Villa Jack Grealish, mai shekara 24, cewa ba shi da damar komawa Manchester United a bazara.(Star)
A bangare guda, ana hasashen cewa Aston Villa za ta dauko dan wasan Marseille -mai shekara 22 dan kasar Faransa Maxime Lopez. (Birmingham Live)
Dan wasan Tottenham da Koriya ta Kudu Son Heung-min, mai shekara 27, na shirin kammala aikin yi wa kasa hidima na mako hudu a kasarsa bayan jinkirin da aka samu a kakar wasa ta bana saboda annobar coronavirus. (Sun)
Dan wasan Manchester City dan kasar Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 28, ya yi gargadi kan raunin da shi da wasu 'yan wasa suka ji don kada jami'an kungiyar su gaggauta neman su koma fagen tamaula. (Telegraph)
Kocin Everton Carlo Ancelotti na sha'awar hadewa da dan wasan Real Madrid dan kasar Colombia mai shekara 28 James Rodriguez, saboda ya taba zama manajansa a kungiyar ta Spain. (Mirror)











