Yadda Drogba ya hada kan Ivory Coast

Asalin hoton, Getty Images
Filin wasa na Al-Merrikh birni na biyu mafi yawan jama'a a Sudan, bayan Omdurman na cikin filayen duniya da ake ruguntsumin raba gardama.
Karamin filin wasan - wanda ake kira da sunan Red Castle ya zama wajen da ake kafa tarihin labarin kwallon kafa mai kayatarwa.
A ranar 8 ga watan Oktoban 2005, Lissafin bai wuce neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a 2006 a saukake ba. Idan Kamaru ta yi nasara a Masar za ta kai gasar kofin duniya kuma karo na shida kenan.
Duk wani sakamako zai bai wa Ivory Coast wadda ke wasa a Sudan da aka bai wa tazarar maki daya damar zuwa gasar kofin duniya - kuma a karon farko.
An yi wa tawagar Ivory Coast ta 2005 da lakabin ''Ma'abociyar nasara'' wadda Didier Drogba ke jan ragama a lokacin da Kolo Toure da Emmanuel Eboue da kuma Didier Zokora ke haskakawa a gasar Premier ta Ingila.
A lokacin Yaya Toure yana taka leda a kungiyar Girka, Olympiakos, amma ana masa kallon kadara ga tawagar.
Tawagar za ta iya fuskantar kowanne kalubale a nahiyar Afirka. Duk da cewar sau biyu tana rashin nasara a hannun Kamaru a wasan neman gurbi, duk da haka ta kusan kai ga ci, bayan da suka shiga filin Sudan da yammaci.
Duk da haka taurarin Ivory Coast na daf da kafa tarihi, bayan da a gida ba a yi tsammanin za su tabuka ba.
A lokacin yakin basasa da aka fara a 2002 ya raba kasar, inda gwamnatin shugaba, Laurent Gbagbo ke mulkar kudanci, yayin da 'yan tawaye karkashin jagorancin Guillaume Soro ke shugabantar arewacin kasar.
Ranar 19 ga watan Satumban 2002 yaki ya barke a kasar, inda 'yan tawaye ke kai wa birane da ke fadin kasar hare-hare.
Tsohon dan wasan tawagar Ivory Coast, Sebastien Gnahore bai manta abubuwan da suka faru a lokacin ba.
"Abu ne marar dadi. Lokacin da na kira 'yar uwata na ji karar harbe-harbe daga wajen gida," in ji shi.
Ya kara da cewar sun buya a karkashin gado kwana hudu, yunwa ce ta sa suka fito daga inda suka buya.
"Abin da na fi damuwa ko iyalai na za su kasance cikin koshin lafiya. Damuwar da nake da ita a kowace rana kenan."
Yakin ya ci gaba da wanzuwa na gajeren lokaci, bayan da kowanne bangare bai amince da rabuwar kai tsakanin Kudanci da Arewaci ba.
Kusan yakin ya zo karshe a lokacin da shekarar 2005 za ta kare, amma fargaba ta karu a 2005. Watakila makomar arewacin Afirka za ta dusashe.
'Yan kwallon zamani na kallon duniya daban da yadda maza da mata ke hange. Kudin da suka samu na canja rayuwarsu, amma 'yan wasan tawagar Ivory Coast a yammcin nan duk da miliyoyin kudin da suke dauka a Turai sun kwan da sanin sakamakon da ake bukata daga gare su.

Asalin hoton, Getty Images
Drogba ya saka hannu kan kwantaragi a Chelsea kan fam miliyan 24 a Yulin 2004 a matsayin dan wasa mafi tsada da aka saya a Burtaniya, Shekara tara da ya yi a Premier ta fayyace kwarewar da yake da ita a fagen kwallon kafa a fanni da dama.
Ko ka kaunace shi ko kuma ka ki shi ya yi abubuwan bajinta a Stamford Bridge babu tantama.
Drogba ya ci kofin Premier hudu da League Cup uku da kuma Champions League. Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce Drogba mai nasara ne zai kuma ci gaba da haka har tsawon rayuwarsa.

Asalin hoton, Getty Images
Drogba ya samu nasarori da yawa, amma kalubalen da ya fuskanta a watan Oktoba a Sudan daban yake da sauran da ya yi a baya.
An take wasa lokaci daya tsakanin Kamaru da Masar a birnin Alkahira na Masar da na Ivory Coast a Sudan.
Ivory Coast ta kwan da sanin babu abin da ya kamace ta illa lashe wannan, bayan da tawagar Sudan ce ta biyu a kasar rukunin da suke ciki.
Minti na 73, Aruna Dindane ya ci wa Ivory Coast kwallo ta biyu sannan ya kara ta uku. Daga baya ne Sudan ta zare kwallo daya.
Can a Masar kuwa Kamaru ce ta fara cin kwallo a minti na 20 da fara tamaula, yayin da Masar ta farke a minti na 79, hakan ya bai wa Ivory Coast damar da take bukata.
Idan aka yi kunnen doki a Masar, ita kuwa Ivory Coast ta yi nasara a kan Sudan to hakan zai kai ta kofin duniya a karon farko.
Daf da za a tashi wasa a Cairo sakamakon wasa na kunnen doki, Ivory Coast na shirin shiga gasar kofin duniya a karon farko kuma a lokacin sun yi nasara a Sudan da ci 3-1, an kuma tashi wasan. Drogba na tsaye tare da sauran tawagar Ivory Coast sun zagaye shi.
Dukkansu suna sauraren sakamakon karawa tsakanin Masar da Kamaru a radiyo suna ta fatan wasan ya kare a kunnen doki, kawai sai aka bai wa Kamaru bugun daga kai sai mai tsaron gida fenariti kuma daf da za a tashi wasan.
Pierre Wome ne ya buga fenaritin, amma sai kwallo ya bugi turken hagu ya yi waje.
A lokacin 'yan wasan Kamaru suka taru a dari'a ta 18 ta Masar suna mamaki, wasunsu sun zazzaro idanu, wasu na figar rigunansu. A wani bangaren kuma kasar Ivory Coast ta barke da murna. A karon farko a tarihi za su je gasar cin kofin duniya a kwallon kafa.
Baki dayan kasar kowanne mutum da kowanne gida na murna. Wannan ranar mun manta cewar kasar na rabe biyu inji Hassane Omar, mai shekara 20 dalibi a birnin Abidjan a wancan lokacin.
Bayan da ake tsaka da murna an shiga da kamara dakin hutawa da sauya kayan 'yan wasa ya cika da jama'a a Al-Merrikh.

Asalin hoton, Getty Images
Nan da nan suka kewaye ta kowanne dan wasa ya dafa kafadar dan uwansa suna tsaye a tsakiyar kamara. A tskiya kuwa dan kwallon Chelsea ne dauke da bututun magana a hannunsa.
Drogba ya yi jawabi ga shugabannin Ivory Coast a lokacin inda ya ce, "ya kamata ku ajiye makamai ku gudanar da zabe."
Ya kuma yi kiran cewar "Maza da matan Ivory Coast daga arewa da kudanci da tsakiya da yammaci mun fayyace a yau duk dan Ivory Coast zai rayu da wasa tare da burin samun gurbin gasar kofin duniya."
"Mun yi muku alkawarin wannan murnar za ta hada kan mutane - a yau muna roko da gwiwowinmu biyu a kasa," nan da nan 'yan wasa gabaki daya a tare suka durkusa.
"Kasa daya a Afirka mai dumbin arziki bai kamata ta fada yaki ba. Ya kamata ku ajiye makamai ku gudanar da zabe." Za ku samu kallon jawabin a Youtube na kusan minti daya wanda ke karewa da lokacin da 'yan wasa suka mike tsaye kan kafafunsu.
Muna son samun nishadi, ku tsayar da harbe-harben bindiga, "daga nan suka shiga rera wakar murna.
Can a gida kuwa an fara bikin murna, akwai rahoton cewar mutane sun je ofishin jakadancin Masar a Ivory Coast domin gode mu su da suka yi canjaras da Masar da ya ba su damar kai wa kofin duniya a karon farko. Hatta birnin 'yan tawaye Bouake ya yi murnar da nasarar da tawagar kasar ta yi.
Duk da adawa, da bajintar su Drogba - an saka wa sunan barasa sunan dan kwallon Chelsea - haka Ivory Coast ta wayi gari a halin da ta ke ciki na rabuwar kasar gida biyu.
Sai dai wani abu ya faru a makon zuwa wata da ya kawo sauye-sauye. An ci gaba da saka faifan bidiyon jawabin Drogba ba dare ba rana kuma hakan ya sa aka samu sauyi, inda bangarori suka kusan cimma yarjejeniya a kan teburi har ta kai ga sa hannu kan tsagaita wuta.

Asalin hoton, Getty Images
Drogba ya bayyana daga jirgin sama wanda ya kwaso tawagar Ivory Coast daga Sudan zuwa gida, kuma kowa na farinciki da bajintar da 'yan wasan suka yi.
A gasar kofin duniya a 2006 an fitar da Ivory Coast a wasannin rukuni, bayan da ta yi rashin nasara a hannun Argentina da kuma Netherlands kafin daga baya ta doke Serbia da Montenegro. An kuma yaba da kwazon Ivory Coast a gasar.
Bayan shekara daya Drogba ya gudanar da wani kasaitaccen jawabi a yankin da 'yan tawaye ke iko a garinsa a lokacin da ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka a wannan shekarar.
Ivory Coast ba za ta buga wasanta a gida da Madagascar ranar 3 ga watan Yuni a 2007 a Abidjan ba kamar yadda aka tsara, amma an kai shi Bouake birnin da 'yan tawaye suke. Wanda wannan wani lamari ne da babu wanda zai ce hakan zai yiwu a shekara biyu baya.
Duk da cewar Drogba yana yankin kudancin kasar inda shugaba Gbagbo yake - ana bauta masa a lokacin.
A lokacin wasa mutane sun yi tururuwa zuwa fili da jami'an tsaro da dama. A cikin fili gwamnati da 'yan tawaye na ta hirar kwallon kafa, kawai an samu sauyi daga tarzomar da ta barke a baya.

Asalin hoton, Getty Images
Tun da 12 na rana kowa ya dakata da aikinsa saboda wasan Ivory Coast, kowa na murna ana ta shaye-shaye kowa na farin ciki.
Daga karshe sai jami'an tsaro ne suka raka Drogba, bayan tashi daga karawar da suka yi nasara da ci 5-0, kuma Drogba ne ya ci kwallon karshe.
Ana tashi daga wasan 'yan kallo suka barke cikin fili, inda jami'an tsaro suka yi wa 'yan wasa katanga saboda tsare lafiyarsu musamman Drogba. Wannan karawar da aka yi a Bouake ta kara hada kan kasa.
Sai dai kuma abin bakin ciki ne ya biyo bayan shekara biyar inda tarzoma ta kara barkewa kan sakamakon zabe, wanda ya janyo mutun 3,000 suka mutu da ta kai aka kama shugaban kasa Gbagbo har aka kai shi kotun duniya don amsa tuhumar cin zarafin aluma.
Tawagar Ivory Coast ta kasa kai bantenta, bayan da ta yi rashin nasara a gasar cin kofin Afirka a wasan karshe a 2006 da kuma 2012.
Drogba ya yi ritaya daga buga tamaula a 2018, bayan nasarorin da ya samu a kasashe shida da ya taka leda, kuma shi da 'yan wasan Ivory Coast an yaba da rawar da suka taka ta hada kan kasa ta fannin kwallon kafa.
Drogba da sauran tawagar kwallon kafar Ivory Coast ba wai sun dakatar da yakin basasa ba ne kadai sun kuma sa fata na gari ta fanni kwallon kafa a kasar.
From: Mohammed Abdu
Sent: 02 April 2020 16:59
To: Awwal Ahmad
Subject: DROGBA FEATURE
Yadda Drogba ya hana yakin basasa a Ivory Coast
Filin wasa na Al-Merrikh a Sudan da ke birni na biyu a yawan mutane, bayan Omdurman daya ne daga wajen da a duniya ake ruguntsumin raba gardama.
Karamin filin wasan - wanda ake kira da sunan Red Castle ya zama wajen da ake kafa tarihin labarin kwallon kafa mai kayatarwa.
A ranar 8 ga watan Oktoban 2005. Lissafin bai wuce neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a 2006 a saukake ba. Idan Kamaru ta yi nasara a Masar za ta kai gasar kofin duniya kuma karo na na shida kenan. Duk wani sakamako kasa da haka zai bai wa Ivory Coast wadda ke wasa a Sudan da aka bai wa tazarar maki daya damar zuwa gasar kofin duniya - kuma a karon farko.
An yi wa tawagar Ivory Coast ta 2005 da lakabin ''Ma abociyar nasara'' wadda Didier Drogba ke jan ragama a lokacin da Kolo Toure da Emmanuel Eboue da kuma Didier Zokora ke haskakawa a gasar Premier ta Ingila.
A lokacin Yaya Toure yana taka leda a kungiyar Girka, Olympiakos, amma ana masa kallon kadara ga tawagar. Tawagar za ta iya fuskantar kowanne kalubale a nahiyar Afirka. Duk da cewar sau biyu tana rashin nasara a hannun Kamaru a wasan neman gurbi, duk da haka ta kusan kai ga ci, bayan da suka shiga filin Sudan da yammaci.
Duk da haka taurarin Ivory Coast na daf da kafa tarihi, bayan da a gida ba a yi tsammanin za su tabuka ba. A lokacin yakin basasa da aka fara a 2002 ya raba kasar, inda gwamnatin shugaba, Laurent Gbagbo ke mulkar Kudanci, yayin da 'yan tawaye karkashin jagorancin Guillaume Soro ke shugabantar Arewacin kasar.
Ranar 19 ga watan Satumba 2002 yaki ya barke a kasar, inda 'yan tawaye ke kai wa burane da ke fadin kasar hare-hare. Tsohon dan wasan tawagar Ivory Coast, Sebastien Gnahore bai manta abubuwan da suka faru a lokacin ba.
''Abu ne mara dadi. Lokacin dana kira 'yar uwata na ji karar harbe-harbe daga wajen gida,''. Ya kara da cewar sun buya a karkashin gado kwana hudu, yunwa ce ta sa suka fito daga inda suka buya.
''Abin da na fi damuwa ko iyalai na za su kasance cikin koshin lafiya. Damuwar da nake da ita a kowace rana kenan.''
Yakin ya ci gaba da wanzuwa na gajeren lokaci, bayan da kowanne bangare bai amince da rabuwar kai tsakanin Kudanci da Arewaci ba. Kusan yakin ya zo karshe a lokacin da shekarar 2005 za ta kare, amma fargaba ta karu a 2005. Watakila makomar Arewacin Afirka za ta dusashe.
'Yan kwallon zamani na kallon duniye daban da yadda maza da mata ke hange. Kudin da suka samu na canja rayuwarsu, amma 'yan wasan tawagar Ivory Coast a yammcin nan duk da miliyoyin kudin da suke dauka a Turai sun kwan da sanin sakamakon da ake bukata daga garesu.
Drogba ya saka hannu kan kwantiragi a Chelsea kan fam miliyan 24 a Ylin 2004 a matsayin dan wasa mafi tsada da aka saya a Burtaniya, Shekara tara da ya yi a Premier ta fayyace kwarewar da yake da ita a fagen kwallon kafa a fanni da dama. Ko ka kaunace shi ko kuma ka ki shi ya yi abubuwan bajinta a Stamford Bridge babu tantama.
Ya ci kofin Premier hudu da League Cup uku da kuma Champions League. Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce ''Drogba mai nasara ne zai kuma ci gaba da haka har tsawon rayuwarsa''.
Drogba ya samu nasarori da yawa, amma kalubalen da ya fuskanta a watan Oktoba a Sudan daban take da sauran da ya yi a baya.
An take wasa lokaci daya tsakanin Kamaru da Masar a birnin Cairo da na Ivory Coast a Sudan. Ivory Coast ta kwan da sanin babu abin da ya kama ceta illa lashe wannan, bayan da tawagar Sudan ce ta biyu a kasar rukunin da suke ciki. minti na 73 Aruna Dindane ya ci wa Ivory Coast kwallo na biyu sannan ya kara na uku. Daga baya ne Sudan ta zare kwallo daya.
Can a Masar kuwa Kamaru ce ta fara cin kwallo a minti na 20 da fara tamaula, yayin da Masar ta farke a minti na 79, hakan ya bai wa Ivory Coast damar da take bukata. Idan aka yi kunnen doki a Masar, ita kuwa Ivory Coast ta yi nasara a kan Sudan to hakan zai kai ta kofin duniya a karon farko.
Daf da za a tashi wasa a Cairo sakamakon wasa na kunnen doki, Ivory Coast na shirin shiga gasar kofin duniya a karon farko kuma a lokacin sun yi nasara a Sudan da ci 3-1 an kuma tashi wasan. Drogba na tsaye tare da sauran tawagar Ivory Coast sun zagaye shi. Dukkansu suna sauraren sakamakon karawa tsakanin Masar da Kamaru a radiyo suna ta fatan su tashi kunnen doki, kawai sai aka bai wa Kamaru bugun daga kai sai mai tsaron gida fenariti kuma daf da za a tashi wasan.
Pierre Wome ne ya buga fenaritin, amma sai kwallo ya bugi turken hagu ya yi waje. A lokacin 'yan wasan Kamaru suka taru a dari'ar ta 18 ta Masar suna mamaki wasu sun zazzaro idanu, wasu ya figar rigunansu. A wani bangaren kuma kasar Ivory Coast ta barke da murna. A karon farko a tarihi za su je gasar cin kofin duniya a kwallon kafa.
Kasar gabaki daya kowanne mutum da kowanne gida na murna. Wannan ranar mun manta cewar kasar na rabe biyu in ji Hassane Omar, mai shekara 20 dalibi a birnin Abidjan a wancan lokacin.
Bayan da ake tsaka da murna an shiga da kamara dakin hutawa da sauya kayan 'yan wasa ya cika da jama'a a Al-Merrikh. Nan da nan suka kewaye ta kowanne dan wasa ya dafa kafadar dan uwansa suna tsaye a tsakiyar kamarar. A tskiya kuwa dan kwallon Chelsea ne dauke da bututun magana a hannunsa.
Drogba ya yi jawabi ga shugabannin Ivory Coast a lokacin inda ya ce ''Ya kamata ku ajiye makamai ku gudanar da zabe, Ya kara da kira cewar ''Maza da matan Ivory Coast daga Arewa da Kudanci da tsakiya da Yammaci mun fayyace a yau duk dan Ivory Coast zai rayu da wasa tare da burin samu gurbin gasar kofin duniya.''
''Mun yi muku alkawarin wannan murnar za ta hada kan mutane - a yau muna roko da gwiwowinmu biyu a kasa, nan da nan 'yan wasa gabaki daya a tare suka durkusa.
''Kasa daya a Afirka mai dunmin arziki bai kamata ta fada yaki ba. Ya kamata ku ajiye makamai ku gudanar da zabe.'' Za ku samu kallon jawabin a Youtube na kusan minti daya wanda ke karewa da lokacin da 'yan wasa suka mike tsaye kan kafafunsu.
''Muna son samun nishadi, ku tsayar da harbe harben bindiga, ''daga nan suka shiga rera wakar murna. Can a gida kuwa an fara bikin murna, Akwai rahoton cewar mutane sun je ofishin jakadancin Masar a Ivory Coast domin gode musu da suka yi canjaras da Masar da ya ba su damar kai wa kofin duniya a karon farko. Hatta birnin 'yan tawaye Bouake ya yi murnar da nasarar da tawagar kasar ta yi.
Duk da adawa, da bajintar su Drogba - an sawa sunan barasa sunan dan kwallon Chelsea - haka Ivory Coast ta wayi gari a halin da take ciki na kasa da ta rabu biyu.
Sai dai wani abu ya faru a makon zuwa wata da ya kawo sauye - sauye. An ci gaba da saka faifan bidiyon jawabin Drogba ba dare ba rana kuma hakan ya sa aka samu sauyi, inda bangarori suka kusan cimma yarjejeniya a kan teburi har ta kai ga sa hannu kan tsagaita wuta.
Droba ya bayyana daga jirgin sama wanda ya kwaso tawagar Ivory Coast daga Sudan zuwa gida, kuma kowa na farinciki da bajintar da 'yan wasan suka yi. A gasar kofin duniya a 2006 an fitar da Ivory Coast a wasannin rukuni, bayan da ta yi rashin nasara a hannun Argentina da kuma Netherlands kafin daga baya ta doke Serbia da Montenegro. An kuma yaba da kwazon Ivory Coast a gasar.
A shekarar gaba Drogba ya gudanar da wani kasaitaccen jawabi a yankin da 'yan tawaye ke iko a garinsa a lokacin da ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka a wannan shekarar.
Ivory Coast ba za ta buga wasanta a gida da Madagascar ranar 3 ga watan Yuni a 2007 a Abidjan ba kamar yadda aka tsara, amma an kai shi Bouake birnin da 'yan tawaye suke. Wanda wannan wani lamari ne da babu wanda zai ce hakan zai yi wu a shekara biyu baya.
Duk da cewar Drogba yana yankin Kudancin kasar inda sgugaba Gbagbo yake - ana bauta masa a lokacin.
A lokacin wasa mutane sun yi tururuwa zuwa fili da jami'an tsaro da dama. A cikin fili gwamnati da 'yan tawaye na ta hirar kwallon kafa, kawai an samu sauyi daga tarzomar da ta barke a baya.
Tun da 12 na rana kowa ya dakata da aikinsa saboda wasan Ivory Coast kowa na murna ana ta shaye-shaye kowa na farin ciki.
Daga karshe sai jami'an tsaro ne suka raka Drogba, bayan tashi daga karawar da suka yi nasara da ci 5-0 kuma Drogba ne ya ci kwallon karshe.
Ana tashi daga wasan 'yan kallo suka barke cikin fili, inda jami'an tsaro suka yi wa 'yan wasa katanga saboda tsare lafiyarsu musamman Drogba. Wannan karawar da aka yi a Bouake ta kara hada kan kasa.
Sai dai kuma abin bakin ciki ne ya biyo bayan shekara biyar inda tarzoma ta kara barkewa kan sakamakon zabe, wanda ya jawo mutun 3,000 suka mutu da ta kai aka kama shugaban kasa Gbagbo har aka kai shi kotun duniya don amsa tuhumar cin zarafin aluma.
Tawagar Ivory Coast ta kasa kai bantenta, bayan da ta yi rashin nasara a gasar cin kofin Afirka a wasan karshe a 2006 da kuma 2012.
Drogba ya yi ritaya daga buga tamaula a 2018, bayan nasarorin da ya samu a kasashe shida da ya taka leda, kuma shi da 'yan wasan Ivory Coast an yaba da rawar da suka taka ta hada kan kasa ta fannin kwallon kafa.
Drogba da sauran tawagar kwallon kafar Ivory Coast ba wai sun dakatar da yakin basasa bane kadai sun kuma sa fata na gari ta fanni kwallon kafa da kasar.











