Manchester United za ta dauko De Ligt, Pogba zai koma Juventus

Asalin hoton, Reuters
Manchester United na shirin sayo dan wasan Juventus da Netherlands Matthijs de Ligt, mai shekara 20, a yayin da dan wasan tsakiya na Faransa Paul Pogba, mai shekara 27, ke tattara kayansa domin barin Old Trafford inda ya nufi Juventus. (Star)
Za a iya tilasta wa Manchester United ta biya dan wasan Chile Alexis Sanchez, mai shekara 31, £1.1m duk shekara idan ya koma daga Inter Milan inda yake can a matsayin aro. (Sun)
Everton ta ware miliyoyin kudi domin sayo dan wasan Real Madrid Gareth Bale, mai shekara 30, da takwaransa na Juventus Aaron Ramsey, mai shekara 29. (90min.com)
A gefe guda, Everton tana yin amfani da manhajar bidiyo ta Zoom domin ci gaba da tattaunawa da 'yan wasa da ma'aikatanta, a yayin da dan wasanta da yake jinya Morgan Schneiderlin, mai shekara 30, yake shirin yin amfani da manhajar wajen tattaunawa da likitansa. (Guardian)
Dan wasan Real Madrid Karim Benzema, mai shekara 32, ya kare kansa kan kalaman da ya yi inda ya kwatanta dan wasan Chelsea kuma abokin aikinsa a tawagar Faransa Olivier Giroud, mai shekara 33, da 'motar tsere' a shafinsa na Instagram. (Marca)
Arsenal na sha'awar sayo dan wasan Ivory Coast Hamed Traore, mai shekara 20, wanda ke zaman aro a Sassuolo daga Empoli, da dan uwansa Amad, mai shekara 17, wanda ke murza leda a Atalanta. (90min.com)






