Rustu tsohon golan Turkiya ya kamu da coronavirus

Rustu Recber

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon mai tsaron ragar tawagar kwallon kafar Turkiya, Rustu Recber yana mawuyacin hali a asibiti saboda coronavirus.

Tsohon dan wasan Barcelona da Fenerbahce daya ne daga 'yan kwallon da suka buga wa Turkiya wasan daf da karshe a gasar kofin duniya a 2002 da suka kai karawar daf da karshe.

Rustu, mai shekara 46, ya yi ritaya daga buga tamaula a 2012, bayan kaka biyar da ya yi a Besiktas.

Fenerbahce ta mika sakon fatan samun sauki ga tsohon dan wasanta a Twitter ''Muna yi wa tsohon dan kwallon Turkiya kuma wanda ya sa mana riga ya kuma wakilce mu shekara da dama fatan samun sauki cikin gaggawa''.

Ita ma Barcelona ta mika fatan alheri ga tsohon dan kwallonta a Twitter ''Muna yi ma fatan alheri, muna kyaunarka, duk 'yan Barcelona na tare da kai''.