Coronavirus: An kara jinkirta wasanni a Ingila sai 30 ga watan Afrilu

EPL

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasan karshe da aka yi a Premier an yi shi ne ranar 9 ga watan Maris

An kara dage wasanni a Ingila har sai ranar 30 ga watan Afrilu saboda ci gaba da yaduwa da cutar coronavirus ke yi a kasar.

Duka wasannin Ingila da suka hadar da Premier Lig, da Championship, da gasar mata ta Super Lig da ta Championship.

Haka zalika an dage duka wasannin a yankunan Scotland da Wales da arewacin Ireland.

Hukumar kwallon kafa ta amince a kara dage kakar wasa ta bana zuwa nan gaba saboda halin da ake ciki.

Karkashin wannan sabuwar yarjejeniyar matsar da wasannin an tsara ci gaba da wasannin ne a ranar 1 ga watan Yuni.

A wata sanarwar hadin gwiwa da hukumar Premier da takwarorinta suka fitar, ta nuna "yadda aka dukufa kan nemam hanyoyin da za a ci gaba da kakar wasanni ta 2019-2020" tare da kammala sauran kananan gasar nahiyar Turai " da zarar an samu damar haka da kuma nutsuwar yin hakan".

Dage gasar Euro 2020 ya ba da damar sauran gasar lig lig da ake bugawa a matsar da ita zuwa watan Yuni.

Haka kuma gwamnatin Burtaniya ta dakatar da duk wasu al'amuran wasanni daga lokacin da aka bayar da shawarar hana taron mutane.

A makon da ya gaba ta ne mataimakin Shugaban kungiyar kwallon kafa ta West Ham Karren Brady ya ce ya kamata a soke kakar wasa ta bana.

Shugaban hukumar FA Greg Clarke ya nuna yanayin da ake ciki da kyar zai bari a kammala wannan kakar.

Sai dai Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Brighton Paul Barber ya shaida wa BBC cewa, zai zama rashin adalci matukar aka hana Liverpool wannan Kofi, ya kuma ba da shawarar a kara kungiyoyin Premier zuwa 22 a shekakar 2021.

Tuni hukumar Fifa ta kafa wani kwamitin da zai yi duba kan matsanancin halin da kwallon kafa ke ciki a duniya.

Da kuma yadda za a gyara matsalar kwantaragin 'yan wasa, wadanda mafi yawa za ta kare nan da 30 ga watanYuni mai zuwa.