Zlatan yana neman taimakon kudin yaki da coronavirus

Zlatan Ibrahimovic

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zlatan ya taka leda a kungiyoyi masu dama ciki har da AC Milan kafin ya kara komawa a karo na biyu

Zlatan Ibrahimovic ya kaddamar da gidauniyar neman taimako domin yakar annobar coronavirus.

Dan wasan ya kuma nemi sauran takwarorinsa da ke buga kwallo a fadin duniya da su hada hannu domin korar wannan cuta.

Dan kwallon dai na taka leda ne a AC Milan a Italiya, kasar da coronavirus ta fi yi wa illa bayan China.

Yanzu dai Ibrahimovic ya tara kudi da suka kai euro 50,000 sau biyu.

Movic ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa "Italiya ta yi mini komai, a wannan lokacin mara dadi ina so na biya wannan kasa da nake so abin da ta yi mini."

Dan wasan Manchester United Paul Pogba ya kaddamar da irin wannan asusun neman tallafin duk a kan wannan cuta.

"Ina fatan abokan kwallona za su taimake ni a kowanne bangare na wasanni wadanda za su bayar da kadan ko mai yawa duk su taimaka a kori wannan cuta.

"Mu hada hannu wajen taimakon asibitoci da likitoci da kuma ma'aikatan asibiti wadanda ba sa gajiya wajen kokarin ceton rayuwarmu saboda a yau mu muke yaba musu!

"Mu hada hannu wuri daya domin yakar wannan cuta mu yi nasara a wasan!"

Sa'a guda bayan Ibrahimovic ya wallafa wannan sanarwa kudin da aka samu suka karu zuwa euro 109,652, kwatankwacin fam 100,999.

A garshen bidiyon da ya wallafa ya ce "ku tuna ion wannan cuta bata je wajen Zlatan ba, Zlatan zai je wurin ta!"