Arsenal ta fitar da rai kan Aubameyang, Chelsea na son dauko Coutinho

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal za ta rasa dan wasanta na gaba Pierre-Emerick Aubameyang mai shekara 30 a wannan bazarar kuma kungiyar tana son fam miliyan 50.7 daga wajen Barcelona da ta nuna sha'awar daukarsa. (Sport, in Spanish)
Borussia Dortmund ta sha gaban Liverpool da Manchester United da Chelsea a rige-rigen sayen dan wasan tsakiyar Ingila Jude Bellingham, mai shekara 16 daga Birmingham a wannan bazarar. (Bild, in German)
Manchester City da Juventus da kuma Paris St-Germain suna sha'awar sayen dan wasan tsakiya dan Faransa Houssem Aouar mai shekara 21 daga Lyon. (Corriere dello Sport, in Italian)
Arsenal sun tattauna da Hammarby kan yarjejeniyar sayen dan wasan kasar Sweden mai shekara 16 Emil Roback, wanda kuma Bayern Munich ke nuna sha'awarsa. (Daily Mail)
Arsenal za kuma ta tattauna da dan wasan tsakiyar Villarreal Santi Cazorla a bazara don ba shi dama ya yi bankwana da magoya baya. Dan wasan mai shekara 35 ya bar kungiyar ne a bazarar 2018, kuma bai yi wasa ba tsawon shekara biyu saboda raunin da ya ji. (Daily Express)
West Ham tana sa ido kan ci gaba da dan wasan Ingila mai shekara 20 Dion Sanderson ke samu, wanda ke wasa aro a Cardiff daga Wolves. (Daily Mail)
Chelsea ta tattauna da Barcelona kan yiwuwar aro Philippe Coutinho dan Brazil mai shekara 27 a kakar wasan badi. (Sport, in Spanish)
A shirye Manchester City da Manchester United suke su sayo dan wasan tsakiya na Spain Saul Niguez, inda dan wasan mai shekara 25 yake kokarin cimma sabuwar yarjejeniya da Atletico Madrid. (Mundo Deportivo, in Spanish)
Inter Milan ta shirya kara tsawon kwantiragin Ashley Young da shekara daya, bayan irin bajintar da ya nuna tun bayan komawarsa kungiyar a watan Janairu daga Manchester United. (Gazzetta dello Sport, in Italian)
Arsenal da Chelsea suna sa ido kan ci gaban da Leon Bailey na kungiyar Bayer Leverkusen ke samu, wanda aka kimanta darajarsa a kan fam miliyan 85. (Daily Express)











