Coronavirus: An dakatar da harkokin wasanni a Ghana

Ghana

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Itama Ghana ta shiga jerin kasashen duniya da suka sanar da dakatar da kwallon kafa saboda cuta

An dakatar da dukkan wasannin kwallon kafa a kasar Ghana saboda annobar coronavirus.

Hukumar kwallon kafa ta kasar GFA ce ta bayyana hakan ranar Lahadi, bayan sanarwar da shugaban kasar Nana Akufo-Addo ya yi, wadda ta yi umarnin dakatar da duk tarukan mutane ciki har da harkokin wasannin.

"Shugaban hukumar kwallon kafa ta Ghana ya bayar da umarnin dakatar da wasanni, da gasanni cikin gaggawa har sai wani lokaci a nan gaba," In ji sanarwar.

Hukumar kwallon kafar ta yi burin ci gaba da wasannin tare da daukar shawarwari daga hukumomin lafiya, sai dai gwamnati ta sanar da dakatar da komai.

Ghana ma dai ta shiga jerin kasashen duniya da suka sanar da dakatar da kwallon kafa saboda cutar.

An dakatar da wasannin share fage na kasashen duniya da za su gudana a karshen watan nan.

Tawagar hukumar kwallon kafa ta Afrika ta je Kamaru a karshen makon jiya, domin tattauanwa kan makomar gasar cin kofin nahiyar Afrika wadda aka tsara gudanarwa a watan Afrilu.

Tawagar za ta mika wa hukumar CAF rahotonta nan da dan wani lokaci.