Chelsea ta ja kunnen Mount da ya killace kansa a gida

Blues

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kungiyar ta Blues na fatan ganin duk 'yan wasanta sun bi ka'idojin da aka shin fida musu

Chelsea ta tunasar da dan wasanta na tsakiya Mason Mount cewa ya kamata ya kebe kansa na tsawon kwana 14 kamar yadda aka shaida masa.

Chelsea ta bayyana hakan ne bayan dan wasan ya sanya hotonsa yana wasa da kwallo a wani wuri da ba cikin gida ba.

A ranar Alhamis ne aka yi wa abokin wasan Mount a kungiyar Callum Hudson-Odoi gwaji aka tabbatar yana dauke da cutar.

Kungiyar ta Blues na fatan ganin duk 'yan wasanta sun bi ka'idojin da aka shimfida musu, kan cewa su kebe kansu matukar sun yi mu'amala da wadanda aka tabbatar yana dauke da cutar.

An dai nuna hoton Mount mai shekara 21, yana wasa a arewacin London da dan wasan kungiyar West Ham Declan Rice.

Sai dai, dan wasan na Ingila Rice mai shekara 21, ba a nemi da ya killace kansa ba a matsayin matakin kariya, kamar yadda aka umarci Mount saboda a kungiyarsu babu wanda aka samu na dauke da cutar.

Rahotanni na nuni da cewa babu labarin sabon wani dan wasan Chelsea da ya kamu da cutar ko kuma ma'aikacin kungiyar.

Dan wasan Ingila da ya kamu da cutar Callum Hudson-Odoi mai shekara 19, a ranar Juma'a ya ce yana samun sauki.

A makon da ya gabata aka wanke duka kayan atisayen kungiyar a matakin kariya daga cutar.