Arsenal na son dauko Partey, Ighalo zai samu gurbin dindindin a Man Utd

Thomas Partey playing for Atletico Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Arsenal na shiri domin sayo dan wasan Atletico Madrid Thomas Partey a bazara. Farashin dan wasan na Ghana, mai shekara 26, ya kai £45m (Telegraph)

Juventus za ta yi gogayya da Arsenal da kuma Tottenham a yunkurin dauko dan wasan Chelsea Willian, ko da yake dan kasar ta Brazil mai shekara 30 zai gwammace ya ci gaba da zama a London. (Tuttosport via Sport Witness)

Phil Neville na duba yiwuwar dauko mai horas da kungiyar kwallon mata ta Ingila bayan da suka sha kaye sau takwas cikin wasa 12 da suka fafata. (Mail)

Arsenal na sa ran za a jinkirta wasanni biyu da za su yi bayan da aka tabbatar cewa kocinsu Mikel Arteta ya kamu da coronavirus. (Mirror)

Kungiyoyin da ke buga gasar Firimiya ba sa son bai wa 'yan wasansu hutun bazara a wannan watan saboda fargabar kamuwa da coronavirus. (Mail)

Uefa da kungiyar kulob-kulob na Turai za su nemi a jinkirta buga gasar Euro 2020 zuwa shekara daya domin su bai wa kungiyoyin kwallon kafar Turai damar kammala gasar da suke yi saboda tsoron coronavirus.(Mirror)

Vitesse Arnhem na sha'awar sayen dan wasan Chelsea dan kasar Ingila mai buga gasar 'yan kasa da shekara 21 Conor Gallagher, mai shekara 20, wanda yanzu haka yake zaman aro (Sun)

Everton na son dauko dan wasan Italiya Andrea Belotti, mai shekara 26, daga Torino. (Calciomercato- in Italian)

Hukumar gasar lig-lig ta Ingila tana goyon bayan West Brom a rikicin da take yi da Barcelona a kan matakin da Barca ta dauka na sayo dan wasan Ingila mai shekara 16 Louie Barry, wanda ya koma Aston Villa. (Express and Star)

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce yana son Odion Ighalo ya zama dan wasansu na dindidin daga matsayin aron da yake a yanzu. Dan wasan Najeriyar mai shekara 30, ya zura kwallo hudu a wasa takwas da ya buga wa kungiyar daga Shanghai Shenhua a watan Janairu.(Manchester Evening News)

Dan wasan Chelsea Hakim Ziyech, mai shekara 26, yana fatan rarrashin kungiyar ta sayo golan Najeriya Andre Onana, mai shekara 23, daga Ajax(Mail)