Coronavirus: 'Yan wasan Leicester City uku da suka nuna alamu sun killace kansu

Asalin hoton, Getty Images
Kocin kungiyar kwallo kafa ta Leicester City Brendan Rodgers ya ce wasu 'yan wasan kungiyar uku sun killace kansu bayan sun nuna alamun kamuwa da cutar coronavirus, kuma tuni aka cire su daga tawagar kungiyar.
Brendan Rodgers bai bayyana wadanne 'yan wasa ba ne suka killace kan nasu ba, amma ya kara da cewa "kungiyar na bin tsarin da aka tanada."
An shirya Foxes za ta buga wasanta na Premier ne da Watford a filin wasa na Vicarage Road a ranar Asabar da karfe 12:45 agogon GMT.
"Muna da wasu 'yan wasa kadan da suka nuna alamun kamuwa da cutar," in ji Rodgers
Zai zama abin kunya {in aka dage wasan Watford}, amma lafiyar al'umma ta fi komai muhimmanci."






