Man City da Man Utd na son sayo Harry Kane, Jadon Sancho zai bar Dortmund

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City da Manchester United za su yi gogayya a yunkurin da suke yi na dauko dan wasan Tottenham Harry Kane, mai shekara 26, a kan £150m a bazara. (90min)
Ita ma Juventus tana son sayo kyaftin din na Ingila Kane a bazara domin murza leda tare da Cristiano Ronaldo. (Tuttosport - in English)
Borussia Dortmund za ta bar Jadon Sancho ya bar kungiyar a bazara idan ya bukaci yin hakan. Liverpool, Manchester United da kuma Chelsea suna zawarcin dan wasan na Ingila mai shekara 19. (Standard)
Chelsea da Tottenham na son sayo golan Bournemouth Aaron Ramsdale, mai shekara 21. (Mail)
Dukkan kungiyoyin suna son sayo Jeremie Boga, mai shekara 23. Kungiyar Sassuol ta kasar Italiya za ta karbi £13m a kan dan kasar ta Ivory Coast kuma tsohon dan wasan Chelsea inda rahotanni suka ce Borussia Dortmund da Valencia ma suna son dauko shi. (Sun)
Arsenal da Tottenham sun shirya domin fafatawa wajen sayo dan wasan RB Leipzig Marcel Sabitzer mai shekara, 25, wanda ya zura wa Tottenham kwallo biyu a wasan Zakarun Turai ranar Talata.(Calcio Mercato - in English)
Tottenham tana kuma son sayo dan wasan Real Madrid Eder Militao. Real na son a ba ta £70m kan dan kasar ta Brazil, mai shekara 22. (El Desmarque - in English)
Pierre-Emerick Aubameyang ya ce yana cike da farin ciki a Arsenal. Ana ta rade radin cewa dan kasar ta Gabon mai shekara 30 zai koma Barcelona. (Mirror)
Bayern Munich na son sayo dan wasan Chelsea, Willian. Kwangilar dan wasan na Brazil, mai shekara 31, za ta kare a Stamford Bridge a bazara. (Sun)
Chelsea za ta yi kokarin sayo dan wasan Porto dan kasar Brazil Alex Telles, mai shekara 27, idan bata yi nasarar sayo Ben Chilwell ba. Dan wasan naLeicester mai shekara 23 shi ne mutumin farko da take son daukowa domin buga mata wasa a baya a kakar wasa mai zuwa. (Star)











