Muhammadu Sanusi II: 'Kaduna mun tsinci dami a kala'

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce tuni Sanusi na II ya karbi sabbin ayyukan da ta nada shi har ma ya kama aiki gadan-gadan don ciyar da jihar gaba.
Kwamishinan harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya fada wa BBC cewa babu wata siyasa a nade-naden da gwamnatinsu ta yi wa tsohon sarki, sai dai fa bisa la'akari da kudurinsa na bunkasa rayuwar al'umma a wannan yanki na arewacin Najeriya.
Sanusi na II ya samu nadin sabbin mukamai daga Gwamna Nasir El-Rufa'i, sa'o'i bayan tube shi daga kan karagar sarautar Kano ranar Litinin.
An nada sarkin mai murabus ne a matsayin mataimakin shugaban kwamitin gudanarwa a hukumar bunkasa zuba jari ta jihar Kaduna, (KADIPA), da kuma mukamin Uban Jami'a ta jihar Kaduna.
Samuel Aruwan ya ce gwawarmayar da ake yi wajen ganin an fitar da al'ummar arewacin Najeriya da ma a Najeriyar gaba daya don fitar da mutane daga halin da ake ciki su ne suka sanya hankalin gwamnatin Kaduna daukar wannan shawara don cin moriyar dabaru da basirar Muhammadu Sanusi.
Ya musanta rade-radin da ake yadawa cewa nada tsohon sarkin kan wadannan mukamai na da alaka da siyasa, inda ya ce alakar da ke tsakanin Gwamna El-Rufa'i da Sanusi na II, dadaddiya ce da ta shafe sama da shekara 40.
Kwamishinan ya ce ganin matsalolin da arewa ke fuskanta da gwagwarmayar neman bunkasa tattalin arziki da ilimi a yankin na daga cikin dalilai da suka yi la'akari da su wajen bai wa Sarki Sanusi Murabus mukamai a Kaduna.
Ya kuma ce ba su ba shi mukaman don watsa wa kowa kasa a ido ba, bisa la'akari da halin da Sanusi II ya shiga tun a farkon wannan mako.
A cewar Mista Aruwan tuni tsohon sarki ya amince kuma ya karbi mukaman da gwamnatin Kaduna ta ba shi, kuma har ma ya fara aiki.
Ko da aka tambaye shi cewa ko sun yi la'akari da cewa tsohon sarkin yana tsare a jihar Nasarawa kafin yi masa wadannan nade-nade? Aruwan ya ce a iyakar sanin gwamnatin Kaduna, gudunmawar da Sanusi II zai bai wa jihar Kaduna, ba aiki ne da sai lallai ya kasance kullum a cikin jihar ba.
"Ai ba aiki ne da ke bukatar kullum sai ya je ofis ba. A duk inda yake (yana iya gudanar da ayyukansa),* in ji shi
Samuel Aruwan ya ce idan aka yi la'akari da kwarewar da kuma mutanen da ya sani gami da abokan alakarsa a fannin tattalin arziki da ilmi, Sanusi II, wata gagarumar dama ce ga jihar Kaduna.
"Duk fa duniya, ana alfahari da shi. duk inda mutum ya je zai ga ana alfahari da shi. A nan nahiyarmu ta Afirka, ana alfahari da shi. Haka ma sauran nahiyar Turai da kasashen Larabawa." In ji Kwamishinan.
Ya ce duk wani abu da ake yi na ciyar da al'umma gaba, idan aka je za a samu sunan Muhammadu Sanusi II a ciki.

Asalin hoton, Muhd photography
Aruwan ya bayyana tsohon sarkin a matsayin jajirtacce kuma zakakuri wanda ana iya kiransa da mikiya mai hangen nesa.
A ranar Litinin ne, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sauke Sarki Sanusi II tare da maye gurbinsa da Aminu Ado Bayero - da ga marigayi Ado Bayero
Muhammadu Sanusi II, basarake ne mai yawan janyo ka-ce-na-ce kuma tun a lokacin mulkin Kwankwaso ya fara kai ruwa rana da gwamnatin jihar, har ta ba shi takardar gargadi karo biyu.
An jima ana takun-saka tsakaninsa da gwamnan Abdullahi Ganduje wanda ake ganin hakan ya kai ga ya rasa rawaninsa.
Yanzu haka dai an killace sarkin a garin Awe da ke jihar Nasarawa, kuma rahotanni na nuna banda iyalansa babu wanda ake bari ya gansa ko ya ziyarce shi.
Mutane da dama dai a Najeriya na cigaba da tofa albarkacin bakinsu kan yadda aka aike tsohon sarkin kauye a jihar Nasarawa.











