Ba ni da tabbas din ci gaba da zama a Madrid – Zidane

Zinedine Zidane

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zidane ya ce maganar tabbas ma babu ita

Bayan doke Barcelona, Real Madrid za ta gwabza da Real Betis a ranar Lahadi kuma koci Zinedine Zidane ya ce "babu tabbas" ko zai ci gaba da zama a kungiyar.

A wani taron manema labarai gabanin wasan na Lahadi, Zidane ya bayyana yanayin girman wasan da tawagar tasa za ta yi.

A baya-bayan nan wasu rahotanni suka alakanta shi da komawa Juventus da kuma tawagar kasar Faransa, saidai ya ce har yanzu ba a tuntube shi ba game da batun.

"Ba a tuntube ni ba kuma ban san komai ba," in ji Zidane. "Ana yawan fadar abubuwa daga waje," kamar yadda jaridar Marca ta ruwaito shi yana fada.

Duk da haka dan kasar Faransan yana ganin babu wanda ya tsira daga kora a yanayin aikinsa na koci.

"Maganar tabbas ma babu ita [a harkar horarwa]. Muhimmin abu shi ne [mayar da hankali] yau da kullum.

"Ina samun goyon baya daga mahukuntan Real madrid, ni ne koci a yanzu amma gobe hakan ka iya canzawa."

Ganin yadda Vinicius Junior ya haskaka a 'yan makonnin nan, ana ganin ya sha gaban Gareth Bale a tawagar. Sai dai Zidane ya ce ba haka abin yake ba.

"Babu wanda ya fi wani. Ina fada masu cewa na yi imanin dukkaninsu suna da amfani saboda dukkansu suna bayar da gudummawa.

"Ni nake yanke hukunci, wanda ba mai sauki ba ne a wurina. Na san yadda 'yan wasan suke tunani, kowa so yake ya buga wasa."

Barcelona wadda ke matsayi na biyu, za ta buga wasan mako na 27 da Real Socieded da karfe 6:30 na yammacin Asabar.

Sai kuma a daren Lahadi Real Madrid ta ziyarci Real Betis da karfe 9:00.