An yi waje da Arsenal a gasar Europa League

Kungiyar Arsenal ta yi ban kwana da gasar Zakarun Turai ta Europa League ta bana.

Arsenal ta yi ban kwana da gasar ce, bayan da Olympiakos ta doke ta da ci 2-1 a Emirates.

Tun farko kungiyoyin sun je hutu bayan minti 45 babu wadda ta zura kwallo a raga.

Bayan da suka koma wasan zagaye na biyu ne Olympiakos ta ci kwallo ta hannun Pape Abou Cisse.

Haka lokaci ya cika an ci Arsenal 1-0, daga nan ne aka yi musu karin lokaci, bayan da a karon farko a Girka, Arsenal ce ta ci 1-0.

Aminti na 113 kyaftin din Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang ya karke kwallo.

Sai dai minti shida tsakani Olympiakos ta kai kora ta kuma zura kwallo a ragar Arsenal.

Jumulla sun tashi kwallo 2-2 a raga kenan, amma zura biyun da aka yi Gunners a gida ne ya sa ta yi ban kwana da wasannin bana.

Kalubalen Arsenal shi ne yadda za ta samu gurbin buga gasar Zakarun Turai ta badi, ko ta Champions League ko ta Europa League.

Kawo yanzu bayan da aka buga wasannin mako na 27 a gasar Premier, Arsenal tana ta tara da maki 37.

Karawar da Arsenal ya kamata ta yi da Manchester City ranar Lahadi 1 ga watan Maris ya zama kwantai.

Manchester City za ta buga wasan karshe da Aston Villa a League Cup ranar Lahadi a Wembley.

Sauran wasannin Premier da suka rage wa Arsenal:

  • Arsenal da West Ham
  • Brighton da Arsenal
  • Southampton da Arsenal
  • Arsenal da Norwich
  • Wolves da Arsenal
  • Arsenal da Leicester
  • Tottenham da Arsenal
  • Arsenal da Liverpool
  • Aston Villa da Arsenal
  • Arsenal da Watford

Ranar 2 ga watan Maris Arsenal za ta ziyarci Portsmouth a wasan gasar FA Cup.