Arsenal ta dauki Pablo Mari

Kulob din Arsenal da ke Ingila ya sanar da daukar dan wasan bayan Sifaniya Pablo Mari a matsayin aro.

Shafin intanet na kungiyar na Arsenal.com ya rawaito cewa dan wasan mai sheara 26 ya murza leda a Flamengo inda ya taimaka wa kungiyar wajen lashe gasar Serie A ta Brazil da kofin (Copa Libertadores) a bara.

Ya taka wa Flamengo leda har sau 22 bayan komawarsa kungiyar a Yulin 2016 daga Manchester United.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dai na fama da matsalar yan baya, kuma da ma an yi hasashen kungiyar za ta dauki dan wasan baya a kakar musayar 'yan wasa da ta soma ci tun farkon wannan wata na Janairu.