Yadda Levante ta jika wa Real Madrid aiki da ci 1-0

An maye gurbin Jose Luis Morales jim kadan bayan ya zura kwallonsa ta biyu a kakar wasan bana

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An maye gurbin Jose Luis Morales jim kadan bayan ya zura kwallonsa ta biyu a kakar wasan bana

Real Madrid ta yi watsi da damar sauko da Barcelona daga saman teburin La Liga a yayin da kungiyar da ke tsakiyar teburin, Levante, ta zura mata kwallo daya, karon farko da ta sha kaye tun watan Oktoba.

Barca, wacce za ta ziyarci Real Lahadi mai zuwa, ta samu karin maki biyu bayan ta doke Eibar da ci 5-0 ranar Asabar.

Real bata tabuka abin kirki ba a yayin da take shirin gwabzawa da Manchester City a gasar Zakarun Turai ranar Laraba.

Levante sun yi watsi da damarmaki amma Jose Luis Morales ya zura kwallo ana daf da tashi daga wasan.

Eden Hazard ya yi watsi da babbar damar da Real ta samu ta cin kwallo kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Zinedine Zidane speaks to Eden Hazard after he comes off injured against Levante

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An fitar da Eden Hazard bayan minti 67 da soma wasa