Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Levante ta jika wa Real Madrid aiki da ci 1-0
Real Madrid ta yi watsi da damar sauko da Barcelona daga saman teburin La Liga a yayin da kungiyar da ke tsakiyar teburin, Levante, ta zura mata kwallo daya, karon farko da ta sha kaye tun watan Oktoba.
Barca, wacce za ta ziyarci Real Lahadi mai zuwa, ta samu karin maki biyu bayan ta doke Eibar da ci 5-0 ranar Asabar.
Real bata tabuka abin kirki ba a yayin da take shirin gwabzawa da Manchester City a gasar Zakarun Turai ranar Laraba.
Levante sun yi watsi da damarmaki amma Jose Luis Morales ya zura kwallo ana daf da tashi daga wasan.
Eden Hazard ya yi watsi da babbar damar da Real ta samu ta cin kwallo kafin a tafi hutun rabin lokaci.