Arsenal ta je ta doke Olympiakos a Europa

Asalin hoton, Getty Images
Alexandre Lacazette ne ya ci wa Arsenal kwallon da ta doke Olympiakos a wasan farko na zagaye na biyu a gasar Europa League na kungiyoyi 32 da suka rage.
A wasan sun kusan tashi babu ci, daga baya ne dan kwallon tawagar Faransa ya samu dama saura minti tara a tashi ya yi amfani da ita.
Haka kuma Lacazette, ya samu wata dama mai kyau tun kan hutu a wata kwallo da ya buga daga yadi na takwas.
Olympiakos ma ta samu damar cin kwallo ta hannun Youssef El-Arabi amma mai tsaron ragar Arsenal, Bernd Leno ya hana ta shiga raga.
Arsenal za ta karbi bakuncin Olympiakos a wasa na biyu a Emirates ranar Alhamis 27 ga watan Fabrairu.
Wasu sakamakon wasannin da aka yi:
- Sporting 3 : 1 Istanbul Basaksehir F.K
- FC Kobenhavn 1 : 1 Celtic
- Cluj - Romania 1 : 1 Sevilla
- Club Brugge 1 : 1Manchester United
- Ludogorets Razgrad 0 : 2 Inter Milan
- Eintracht Frankfurt 4 : 1 Red Bull Salzburg
- Shakhtar Donetsk 2 : 1 SL Benfica
- Wolverhampton Wanderers 4 : 0 Espanyol
- Bayer 04 Leverkusen 2 : 1 FC Porto
- Apoel Nicosia 0 : 3 FC Basel 1893
- AZ Alkmaar 1 : 1Lask Linz
- VfL Wolfsburg 2 : 1 Malmo FF
- AS Roma 1 : 0 KAA Gent
- Glasgow Rangers 3 : 2 Sporting Braga







