Barca za ta nemi Aubameyang, City na son sayen Messi

Asalin hoton, Getty Images
Daraktan wasannin Barcelona Eric Abidal ya ce kulob din zai yi bakin kokarinsa na ganin ta sayi dan wasan gaban Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 30, a bazara mai zuwa.(Mirror).
Manchester City ta ce ta shirya tsaf don taya Lionel Messi idan dan wasan dan kasar Argentina mai shekara 32 ya zabi kawo karshen zamansa a Barcelona, idan kwantaraginsa ya kare a karshen kakar wasannin bana.(Manchester Evening News).
Barcelona da Real Madrid sun bi sahun Manchester United wajen zawarcin dan wasan Aston Villa da Ingila Jack Grealish, mai shekara 24. (Sun)
Wolves ta bayyana cewa a shirye take ta kulla yarjejeniyar din-din-din da dan kasar Spain, Adama Traore, mai shekara 24, idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallon kafa a lokacin bazara.(Telegraph).
Chelsea da Manchester za su gwabza wurin neman sayo dan wasan gaban Borussia Dortmund Jadon Sancho, mai shekara 19.(Sun).
Haka kuma kungiyoyin biyu za su fafata wurin kulla yarjejeniya da dan wasan gaban Lyon da Faransa Moussa Dembele. (Mirror).
Tsohon dan wasan tsakiyar Tottenham Christian Eriksen ya ce an mayar da shi saniyar ware a kungiyar tun bayan da ya bayyana ra'ayinsa na barin kungiyar.
KocinArsenal Mikel Arteta yana son sayo 'yan wasan tsakiya biyu da dan wasan gaba daya idan aka fara musayar 'yan wasa a bazara kafin a soma gasar cin kofin Turai, wato Euro 2020. (Mail)
FatanLiverpool da Manchester Unitedna sayo dan wasan Bayer Leverkusen da Jamus Kai Havertz, 20, zai ta'allaka ne makomar dan kasar Brazil Philippe Coutinho a Bayern Munich. (Mirror)











