Pogba na shirin barin United, VAR na ci gaba da shan suka

Dan wasan tsakiyar Manchester United Paul Pogba ya bayyana wa abokan wasansa cewa ba ya sha'awar ci gaba da buga wasa a kungiyar, kuma yana son ya kara gaba da zarar an kammala kakar wasannin da ake ciki. (Manchester Evening News).
Juventus na shirin neman dan wasan Manchester City da Jamus Leroy Sane a badi.
Bayern Munich ce ta fara bayyana sha'awar sayo dan wasan.(Calcio Mercato, via Inside Futbol).
Chelsea ta shirya bai wa mai horar da kungiyar Frank Lampard Fam miliyan 150 domin sayen 'yan wasa a badi, kuma tuni kungiyar ta kyalla ido kan dan wasan gaban Lyon na Faransa Moussa Dembele.(Evening Standard).
Mai horar da 'yan wasan Manchester City Pep Guardiola na bukatar sayen masu tsaron baya guda biyu a kakar badi, wanda hakan ya sa an fara shakku kan makomar mai tsaron bayan Ingila John Stones. (Times, subscription required).
Kungiyoyin Arsenal da Everton za su ci gaba da neman mai tsaron bayan Lille dan kasar Brazil Gabriel duk da sun kasa cimma matsaya kan farashinsa. (Le10 Sport, via Team Talk).
Bincike ya nuna cewa kashi biyu bisa uku na magoya baya a gasar Firimiya ba sa jin dadin aikin na'urar da ke taimakama alkalin wasa ta VAR.
Ejan din Gareth Bale ya musanta cewa Tottenham ta taya dan wasan a watan Janairun da ya wuce da nufin dawo da shi kungiyar. (Talksport)
Masu tsaron gidan Manchester United Sergio Romero dan kasar Argentina da kuma Lee Grant za su bar kungiyar idan an kammala kakar bana. (Sun).
Bournemouth na son dan wasan gabanta Josh King ya sabunta kwantiraginsa, bayan rushewar yarjejeniyar da ya so kullawa da Manchester United dab da rufe kofar cinikin 'yan wasa.(Telegraph).
Tsohon mai horar da 'yan wasan West Ham ya bayyana cewa rashin tabuka abin arziki daga mai tsaron raga Roberto ya taimaka wurin sallamarsa daga aiki.(Evening Standard).
A gasar cin kofin Ingila na FA Liverpool ta doke Shrewbury da ci daya mai ban haushi a Anfield.
Wasan zagaye na biyu ne, bayan da kungiyoyin suka tashi 2-2 a zagayen farko.
Liverpool ta yi amfani da matasan 'yan wasanta ne da nufin bai wa manyan 'yan wasanta damar hutawa.
Hatta mai horar da 'yan wasan kungiyar Jurgen Klopp bai halarci wasan ba.











