Lampard zai raba gari da Kepa, Madrid na shirin sayen Lingard

Asalin hoton, EPA
Kocin Chelsea Frank Lampard yana ta musayar yawu da masu kulob din domin sayar da mai tsaron raga Kepa Arrizabalaga, mai shekara 25. (Mirror)
Lampard yana son maye gurbin Arrizabalaga da mai tsaron ragar Burnley da Ingila Nick Pope, dan shekara 27. (Express)
Dan wasan tsakiya na Ingila James Maddison, mai shekara 23, na dab da sanya hannu a sabon kwantaragi a Leicester. (Telegraph)
Atletico Madrid da Roma na cikin 'yan gaba-gaba da ke son sayen dan wasan tsakiya na Ingila Jesse Lingard, mai shekara 27, idan ya bar Manchester United. (ESPN)
Liverpool, Manchester United da Chelsea na zawarcin Timo Werner, mai shekara 23, wanda ya ce zai koma kulob din da ya kwanta masa a rai. Dan wasan dan kasar Jamus ya zura kwallo 25 a dukkan gasar da ya buga wa RB Leipzig a kakar wasa ta bana. (Kicker - via Evening Standard)
'Yan wasan Manchester City sun bukaci kocinsu Pep Guardiola ya daina saurin sauya 'yan wasan da yake soma sanya wa a tamaula bayan sun sha kashi a hannun Tottenham ranar Lahadi. (Mail)
Mai yiwuwa dan wasan gaba naReal Madrid da Wales Gareth Bale, mai shekara 30, zai koma kulob din kasar China da ke buga gasar Super League ko Major League Soccer, maimakon kulob din da ke buga gasar Firimiya, idan ya bar Madrid. (Star)
Arsenal da Everton basu yi nasara ba a yunkurinsu na sayen dan wasan Lille dan kasar Brazil Gabriel, mai shekara 22, a watan Janairu. (Le10Sport - in French)
Dan wasan Paris St-Germaindan kasar Faransa, Kylian Mbappe, mai shekara 21, ba zai yi amfani da sabanin da suka samu kwanakin baya da Thomas Tuchel domin barin kulob din ba, in ji kocin. (Goal)
A shirye kulob din Real Madrid yake ta yi zawarcin Mbappe mai shekara 21. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Manchester United ya duba yiwuwar sayo dan wasan Brighton Glenn Murray, mai shekara 36, a lokacin cinikin 'yan kwallon kafa a watan jiya. (Mail)
Kocin Wales kuma tsohon dan wasan Manchester United Ryan Giggs sabon dan wasan da suka saya dan kasar Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 25, zai iya zamar musu alakakai idan aka sanya shi domin buga wasa a bayan kulob din. (Sun)
Liverpool na zumudin sayo dan wasan Netherlands Virgil van Dijk, mai shekara 28, da kuma mai tsaron ragar Brazil Alisson, mai shekara 27. (Independent)










