Ansu Fati mai kafa tarihi a fannin kwallon kafa

Asalin hoton, Getty Images
Ansu Fati ya ci gaba da kafa tarihi a fagen kwallon kafa a karawar da ya zura wa Levante kwallo biyu a gasar La Liga ranar Lahadi.
Barcelona ta yi nasarar doke Levante 2-1 a wasan mako na 22 da suka kara a Camp Nou.
Kwallaye biyun da Fati ya ci sun sa ya zama matashin dan wasa da ya zura biyu a raga a gasar La Liga.
A ranar ta Lahadi yana da shekara 17 da kwana 94 da haihu, ya kuma doke bajintar da Juanmi ya yi a 2010 a Malaga mai shekara 17 da kwanaki 115.
Matashin dan wasan Barcelona da ya ci mata kwallo biyu shi ne Bojan Krkic a fafatawa da Valladolid a 2008 mai shekara 17 da kwanaki 2008 a lokacin.
Tarihin da Ansu Fati ya kafa
- Kawo yanzu yana da kwallo biyar da ya ci wa Barcelona a karawa 18 da ya yi mata, kuma hudu a gasar La Liga, kuma wadan da ya ci sun hada da Osasuna da Valencia da kuma Levante.
- Matashin dan wasan Barcelona da ya ci kwallo a La Liga a karawa da Osasuna yana mai shekara 16 da kwanaki 304.
- Matashin dan kwallon da ya fara buga gasar La Liga, mai shekara 16 da kwana 298.
- Mako biyu tsakani da ya ci Osasuna ya zama matashin da aka fara wasan La Liga da shi ya kuma ci Valencia, yana da shekara 16 da kwana 318.
- Matashin da ya fara buga Champions League a wasan da Barcelona ta yi da Borussia Dortmund, yana da shekara 16 da kwana 321.
- Kwallon da ya ci Inter Milan ya zama matashin dan wasa da ya zura kwallo a Champions League, mai shekara 17 da kwana 40.






