Barca za ta maye gurbin Suarez, Aguero zai bar Man City

Suarez

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami da ke Amurka ta tuntubi wakilan dan wasan Manchester City, Sargio Aguero dan asalin Argentina mai shekara 31.

Ba wai Aguero kadai ba, har ma da dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafar ta Manchester City David Silva da ake sa ran zai bar kungiyar a karshen kakar nan. (The Sun)

Akwai yiwuwar Manchester United ta sayi dan wasan bayan Portugal, Bruno Fernandes mai shekaru 25 a farashin Euro miliyan 55 nan da karshen makon nan (Mirror)

Kulob din Tottenham ya soma takara da Manchester United da kuma Chelsea wajen daukar dan wasan bayan Faransa wato Boubakary Soumane mai shekara 20 (L'Equipe, via Sun).

Manchester United ta mika tayin Euro miliyan 30 don daukar dan wasan bayan Birmingham mai shekara 16 Jude Bellingham (Sun)

Mai horar da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barecelona Quique Setien ya ce kulob din ya soma neman dan wasan da zai maye gurbin Luis Suarez da yaji rauni (Sport)

Barca na kwadayin daukar dan wasan gaban Andulus Rodrigo Moreno da ke murza leda a Valencia, sai dai ana ganin zai kai farashin Euro miliyan 60 (Marca)

Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ta yi gum, a kan maganar dawowar dan wasan gaban ta Islam Slimani wanda yanzu haka ke buga kwantaragin aro a Monaco, abin da ya janyo tarnaki ga aniyar Tottenham ta soma neman dan wasan a wannan watan (Leicester Mercury).

Dan wasan bayan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Alvaro Odriozola ya isa Jamus a kokarin kammala duba lafiyarsa a Bayern Munich da taka leda a matsayin dan wasan aro (AS - in Spanish).

An danganta Barcelona da daukar dan wsan gaban Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang kafin karewar kwantaraginsa a 2021 (Star).

Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City na bibiyar Traore mai shekara 24 dan asalin Burkina Faso da a yanzu haka ke murza leda a Westham. Foot Mercato - in French)

Dan wasan Manchester United Tahith Chong mai shekara 20 ya soma tattaunawa da Inter Milan bayan karewar wa'adinsa da United, yayin da su ma kungiyoyin Barcelona da Juventus suka nuna sha'awarsu ta daukar dan wasan.