Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Premier League: Mourinho ya ci wasan Premier na farko a gida
Tottenham ta samu nasarar ta ta biyu a jere a gasar Premier tun bayan da Jose Mourinho ya karbi ragamar jagorancin kungiyar.
Dele Alli ne ya jefa kwallo biyu a minti na 21 da kuma na 50, abin da ya bai wa kungiyar damar samun nasara uku a jere cikin wasa uku karkashin jagorancin Mourinho kuma nasara biyu da ta yi a jere a kakar bana.
Sai dai an zira wa Tottenham kwallo a dukkanin wasannin.
Sakamakon ya dago kungiyar a teburi, inda ta dawo cikin goman farko. Wasannin gobe ne za su tabbatar da matsayinta a teburin amma yanzu tana ta biyar.
Moussa Sissoko ne ya kara ta uku da watsiya bayan da Son ya ba shi kwallon - ita ce kwallon farko da Moussa Sissoko ya ci cikin wasa 69 da ya buga tun bayan wadda ya ci Huddersfield a watan Afrilun 2017.
A minti na 73 ne dan wasan Bournemouth din Harry Wilson ya farke kwallo daya da aka ci kungiyarsa, sai kuma a minti na 90 ya kara farke dayar, abin da ya sa hantar 'yan Tottenham ta kada.
Duk da cewa Bournemouth ta yi yunkuri sosai a karshen wasan amma dai Tottenham ta samu nasarar lashe maki ukunta da kyar.