Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Premier League: Chelsea ta yi barin maki 6 a jere a Premier
Chelsea ta barar da maki shida a jere a gasar Premier bayan West Ham ta cinye ta har gida da ci 1-0 a wasan mako na 14.
Kungiyar ta Lampard ita ce ta rike kashi 70% na wasan tun daga farko har karshe. Sai dai ba ta samu nasarar zira kwallo ko daya ba.
A minti 45 na farko an buga wasan babu ci, sai dai a minti na 3 da dawowa zagaye na biyu dan wasan bayan West Ham Aaron Cresswell ya zira kwallon tilo da aka yi nasara da ita.
Wannan ce nasara ta farko da West Ham ta samu cikin wasa uku da ta buga a Premier kuma nasara ta farko da ta samu cikin shekara 17 a gidan Chelsea a wasan hamayyar birnin Landan.
A minti na 70 ne dan wasan gaban West Ham Michail Antonio ya kara kwallo ta biyu a ragar Chelsea, sai dai bayan duba na'urar VAR an gano ya taba kwallon da hannu kuma alkalin wasa ya kashe ta.
Wannan nasara kamar ruwan sanyi ce ga wutar da take yunkurin cinye mai horarwa Manuel Palagrini, ganin irin kashin da kungiyar ta sha a baya-bayan nan.
Rahotanni sun ce mahukuntan kulob din sun fara tattaunawa kan makomar kocin amma sun ce za su daga masa kafa.
A bangaren Chelsea kuwa wannan ce rashin nasara ta uku a jere da ta yi, bayan kashin da ta sha a hannun Mancester City da ci 2-1 da kuma canjaras da Valencia a gasar Zakarun Turai ta Champions League a tsakiyar mako.
Chelsea na da maki 26, abin da ya sa har yanzu take cikin cikin jerin kungiyoyi hudun farko - ita ce ta hudun.