Zidane ya bukaci magoya baya su daina nuna kyama ga Bale

Gareth Bale yayinda yake murnar kwallon da Real Madrid ta zura

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Bale ya ci yo wa Real Madrid kwallaye 104 - amma kwallaye biyu ya zura a bana

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce ya kamata magoya bayan kungiyar da ke Sifaniya su daina nuna kyama ga dan wasa Gareth Bale.

'Yan kwallo sun yi wa dan wasan na Wales ihu bayan da aka canja shi a wasan da kungiyarsa ta samu galaba a kan Real Sociedad da ci 3-1.

Wasansa na farko ke nan a Real Madrid tun bayan makonni bakwai da ya dauka ba ya buga mata wasa.

A baya-bayan nan ne dai aka ga Gareth Bale dan kasar Wales da sauran abokan wasansa a tsakiyar fili bayan wasa da ya buga wa kasar dauke da tutar da aka rubuta 'Wales. Golf. Madrid. In that order'.

"Ce-ce-ku-cen ya yi yawa a kan Bale. Yana son ya kasance tare da mu domin ba da gudunmawa," in ji Zidane.

"Ina fatan wannan ba zai ci gaba ba, a sauran kakannin wasan.

"Muna son magoya bayan mu su ba mu hadin kai tun daga farko har karshe, amma da alama ba za mu iya shawo kansu nan da kankanin lokaci ba."

Zidane ya kara da cewa: "Har yanzu ban yi magana da shi akan abin da magoya bayan mu suka yi masa, kawai dai na taya shi murnar ba da gudunmawar da yake yi.

"Ba zan iya cewa abin da ake yi ya dace ko kuma akasin hakan ba. Kowa yana da damar da zai fadi albarkacin bakinsa."

Bale ya juri matsin lamba daga Bernabeu tun daga lokacin da ya koma kulob din daga Tottenham a shekarar 2013, duk da kokarin da ya yi na taimakawa Madrid din lashe kofin gasar Zakarun Turai har sau hudu.

A watan Yuli saura kadan ya rage dan wasan ya koma kulob din Jiangsu Suning da ke kasar China, yayin da mai horarwa Zidane ke cewa ficewar dan wasan daga kungiyar abu ne da ya dace.

Sai dai daga bisani aka ji janyewar tafiyarsa lokacin da Madrid din ta bukaci a biyata diyyar sauya sheka.

Bale ya yi kokarin sake gina kansa a Kulob din, sai dai ya koma Sifaniya lokacin da yake fama da rauni a watan Oktoba, bayan da ya ciyowa kasar sa Wales kwallo a wasanta da Croatia.

Bai sake buga wasa ba, sai a lokacin da Wales ta yi wasa da kasashen Azerbaijan da Hungary.

Bale ya fuskanci ihu daga magoya bayan kungiyar lokacin da aka sanar cewa zai shiga fili a wasan da kungiyar ta yi ranar Asabar.

Dan wasan, mai shekara 30, ya fuskanci makamancin hakan lokacin da aka gabatar da shi daga benci bayan minti 67 da fara wasan Madrid din.

Tun ranar biyar ga watan Oktoba dan wasan bai sake takawa kungiyar leda ba, sai a wasan ranar Asabar din, kodayake ya samu goyon baya daga bisani bayan da ya bayar da gudunmawa sosai a wasan yayin da ya kare matakinsa da kuma taimakawa aka ci kwallo.

Dan wasan shi ne ya taimaka wa Modric ya zura kwallo ta uku a raga.

"An sanya shi cikin tawagar kungiyar kuma yana son buga wasa, kamar kowa," in ji Zidane.

"Jama'a na da 'damar yin abin da suka ga dama, amma na bukace su da su rika yaba wa kowa. Ina mai farin ciki da wasan, da kuma gudunmawar da Bale bayar a wasan."

A ranar Talata ne Real Madrid za ta karbi bakuncin Paris St-Germain.