Premier League: Liverpool ta lallasa Crystal Palace

Asalin hoton, @LFC
Har yanzu tawagar Jurgon Klopp na ci gaba da bai wa kungiyoyi kashi a Premier bayan ta lallasa Crystal Palace har gida da ci 1-2 a wasan mako na 13.
Palace ta bai wa Liverpool wuya sosai domin kuwa ta fi ta taka rawar gani a wasan, inda Liverpool din ta fi shan wahala sama da wasanta da Aston Villa a wasan mako na 11.
Sadio Mane ne ya fara jefa kwallo a ragar masu masaukin bakin a minti na 49 - shi ne dan wasa na uku da ya ci kwallo a wasan Premier biyar a jere a tarihin Liverpool.
Sai ana saura minti takwas a tashi daga wasa Wilfred Zaha ya farke kwallon amma Roberto Firmino bai bari an tashi ba sai da ya kara ta biyu a minti na 85.
Kwallon da Zaha ya ci ita ce ta farko a cikin wasa 14 na Premier da ya buga.
Liverpool ta ci gaba da zamanta a saman teburi da maki 37, maki takwas kenan tsakaninta da Leicester City a matsayi na biyu.






