Man Utd da Gareth Bale? Suarez zai koma MLS

Asalin hoton, Reuters
Akwai yiwuwar Gareth Bale na Real Madrid zai tafi Manchester Utd. (Talksport)
Crystal Palace na son sayen dan gaban Chelsea Olivier Giroud mai shekaru 33. (Express)
Duk da zuwan Jose Mourinho Tottenham, akwai alamun dan wasan tsakiya Christian Eriksen ba zai tsaya ba. (Mail)
Roman Abramovich ya musanta rahotannin da ke cewa zai sayar da Chelsea. Abokansa sun ce Abramovich ya kara son kungiyar ganin yadda tsohon dan wasan kungiyar Frank Lampard ya ke tafiyar da ita (Telegraph)
Dan wasan gaba na kungiyar Barcelona Luiz Suarez ya ce watakila ya koma buga wasa a gasar Major League ta Amurka. (ESPN)
Bayern Munich na shirin fara tattaunawa da Mauricio Pochettino bayan da Tottenham ta sallame shi a wannan makon. (Metro)
Damar da Manchester United da Arsenal da wasu manyan kungiyoyi ke da ita ta sayen dan wasan gaba na Red Bull Salzburg Erling Haaland ta subuce, bayan da aka gano cewa RB Leipzig ta fi kowa damar mallakar dan wasan idan har tana da ra'ayi kan kudi fam miliyan 25. (Sport Bild, daga jaridar Sun)






