Real Madird: 'Yan Madrid sun yi wa Bale ihu a Bernabeu

Asalin hoton, Getty Images
Magoya bayan Real Madrid na ta cecekuce kan Gareth Bale bayan ya shigo wasan da Real din ta lallasa Real Sociedad da 3-1 a wasan La Liga mako na 14 a filin wasa na Bernabéu.
A tsakiyar mako ne dai aka ga Bale dan kasar Wales da sauran abokan wasansa a tsakiyar fili bayan wasa da ya buga wa kasar ta dauke da tutar an rubuta 'Wales. Golf. Madrid. In that order'.
Rubutun yana lissafa abubuwan da Bale ya fi kauna ne wato: ya fi son buga wa kasarsa Wales wasa sannan wasan Golf kafin Real Madrid. (Wales, Golf. Madrid. A jere)
Magoya bayan Real Madrid sun yi wa sunan dan wasan gaban ihu bayan an sanar da sunayen 'yan tawagar da za su buga wasan ana gab da take wasa.
Sun sake yi masa ihun a lokacin da aka taso shi daga benci a minti na 67 - wasansa na farko kenan tun ranar 5 ga watan Oktoba.
Bale ya fuskanci kakkausar suka daga kafafen yada labarai a kasar Spain bisa abin da ya aikata yayin da ya taimaka wa Wales ta samu gurbin shiga gasar Euro 2020 ta kasashen nahiyar Turai.

Asalin hoton, Getty Images
Karim Benzema ne ya farke kwallon da Willian Jose ya jefa a ragar Madrid a minti na 37 kafin Valverde ya kara ta biyu, sai kuma Modric da ya kara ta ukun.
Tun farko dai Barcelona ce ta fara cin wasanta a gidan Leganes.
Yanzu Barcelona da Real Madrid ne ke saman teburin La Ligar da maki 28 kowaccensu, sai Atletico Madrid da take biye masu da maki 25.
Koci Zinedin Zidane ya dage kan cewa ba sai an ci gaba da tattauna lamarin ba kuma bayan tashi daga wasan Bale ya samu goyon baya.
An rika tafa masa bisa taimakon da ya bai wa Luka Modric yayin cin kwallo ta uku da kuma kokarinsa na tsare gida.
Yanzu hankali ya karkata kan gasar Champions League yayin da Madrid din za ta karbi bakuncin Paris St-Germain ranar Talata da karfe 8:00 na dare.











