Euro 2020: Ingila za ta yi wasa da Denmark

Ingila za ta yi wasa sada zumunci hudu kafin zagayen karshe na wasan neman gurbin shiga gasar Euro 2020, ciki akwai wasan da za ta yi da Denmark a Wembley.

'Yan wasan Gareth Southgate zasu fafata da na Danes - wadanda suka samu gurbin zuwa Euro 2020 bayan da suka yi canjaras da Jamhuriyar Ireland - ranar, 31 ga Maris.

Wasan farko-farko zai kasance ranar 27 ga Maris a Wembley. Sai kuma wani wasan da za ta karbi bakuncin sa a watan Yuni.

Za a buga wasan karshe a wani wuri da ba a bayyana ba, amma a Turai.

Ingila ta buga wasa da Denmark a wasan sada zumunci a 2014 kuma ba ta sha kaye a hannun kasar ba tun 2005.

Za a yi wasan rukuni na gasar Euro 2020 a Bucharest ranar, 30 ga Nuwamba.

Wasan zagaye na farko da Ingila za ta yi zai kasance ranar, 14 ga watan Yuni. Kuma dukkanin wasannin rukuni-rukunin ta za a buga ne a Wembley.