Arsenal za ta sayar da Xhaka, City za ta sayi Upamecano

Asalin hoton, Getty Images
An bai wa kocin Arsenal Unai Emery wata daya domin ya tsira da aikinsa. (Sun)
Manchester City na duba yiwuwar sayen dan wasan bayan kungiyar RB Leipzig Dayot Upamecano, mai shekara 21 a watan Janairu. (90 Min)
Barcelona ta yi watsi da tayin da wata kungiyar Premier ta yi mata na sayen dan wasan tsakiya dan Croatia Ivan Rakitic kan kudi kusan fam miliyan 13, kasa da fam miliyan 17 da suka yi masa kima. (Sport)
Arsenal za ta sayar wa Borussia Monchengladbach Granit Xhaka mai shekara 27, a wani bangare na wata yarjejeniya da suke son kullawa ta musaya da Denis Zakaria dan kasar Switzerland. (Mirror)
Manchester United za ta yi kokarin sayen dan wasan gaban Norway Erling Braut Haaland mai shekara 19, daga Red Bull Salzburg a watan Janairu, ta kuma bayar da aronsa ga kungiyar Austriyan a sauran kakar bana. (ESPN)
Crystal Palace tana taya dan wasan gaban kungiyar Celtic ta Odsonne Edouard mai shekara 21, kan fam miliyan 20. (Sun)
Real Madrid da Barcelona za su iya neman dan wasan bayan Inter Milan da kasar Slovakia Milan Skriniar, mai shekara 24, wanda kuma Manchester United ma ke nema. (Corriere dello Sport)
Manchester United da Arsenal suna sa ido kan mai tsaron gidan Hartlepool mai shekara 17, Brad Young. (Sun)

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta shirya don tattauna wa da wakilan Tahith Chong, a yayin da kungiyar take sha'awar taya dan wasan tsakiyar dan kasar Netherlands mai shekara 19 daga Juventus. (Metro)
Chelsea na sha'awar dan wasan kungiyar Wigan mai shekara 17 Joe Gelhardt, wanda Manchester United da Manchester City da Liverpool da Tottenham da Everton duk suke sa ido a kansa. (Star)
Dan wasan gaban Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 34, ya ce ba shi da matsala da kocinsa Maurizio Sarri sakamakon sauya shi da ya yi. (Corriere dello Sport)
Daraktan kwallon kafa Eric Abidal ya tabbatar da cewa Barcelona na sha'awar sayo dan wasan gaban Inter Milan da Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 22, domin yiwuwar maye gurbin dan wasan gaban Uruguay Luis Suarez, mai shekara 32. (Mundo Deportivo)
Dan wasan gaban Chelsea dan kasar Belgium Michy Batshuayi, mai shekara 26, yana son ya tsaya don kwatar matsayinsa maimakon barin kungiyar a watan Janairu. (Sun)











